Ku yaki yan majalisa akan mahaukatan kudade da ake biyansu – Balarabe Musa ga yan Najeriya

Ku yaki yan majalisa akan mahaukatan kudade da ake biyansu – Balarabe Musa ga yan Najeriya

Wani tsohon gwamnan jihar Kaduna, Alhaji Balarabe Musa, yayi kira ga yan Najeriya da su yaki mambobin majalissan dokokin kasa na tara sannan su nemi cewar su yanke albashin su.

Yace babu yanda za ayi kasar ta cigaba da biyan yan majalisa makudan kudaden da suke karba.

Musa ya bayyana cewa lamarin ya fi karfin roko, cewa rokon yan majalisa kan su fahimci cewa tattalin arzikin kasa ba zai cigaba da biyan wadannan makudan kudade ba bazai yi wani tasiri ba.

Ya tuna cewa a baya yunkurin da tsohon shugaban kasa Shehu Shagari yayi akan yan majalisan na wancan lokacin akan irin wannan lamarin ya kusa kai sa ga rasa kujeransa saboda barazanar tsige shi da aka yi a lokacin.

Ku yaki yan majalisa akan mahaukatan kudade da ake biyansu – Balarabe Musa ga yan Najeriya

Ku yaki yan majalisa akan mahaukatan kudade da ake biyansu – Balarabe Musa ga yan Najeriya
Source: UGC

Musa yace, “Yanzu, lamarin ya munana. Haka zalika, ba zan bukaci yan Najeriya su roki yan majalisa ba. Su hada kawunansu sannan su tunkari yan majalisan.

KU KARANTA KUMA: Zababbun sanatoci 5 na zawarcin kujerar mataimakin Shugaban majalisar dattawa (jerin sunaye)

“Su yake su. Idan basu yake su ba, yan kadan daga cikin mutanen zasu yashe hakkin yawancin mutane. Yawancin jihohi suna a tsaka mai wuya wajen biyan albashin ma’aikata. Duk da haka kadan daga cikin yan majalisan na cin hakkin al’umman kasar. Muddin muna son cigaban kasar, dole a daina hakan.”

Musa har ila yau yayi kira ga RMAFC da ta “yi abunda ya kamata” wajen rage yawan albashin yan majalisan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Ku fa'idantu da manhajar mu ta Azumi a wannan wata mai albarka a wannan shafi: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel