Garin dadi da nisa: Wani sarki ya saka doka akan mazajen kasarsa da su dinga auren mata a kalla guda hudu

Garin dadi da nisa: Wani sarki ya saka doka akan mazajen kasarsa da su dinga auren mata a kalla guda hudu

- Sarkin kasar Swaziland ya saka dokar auren mata akalla guda biyar ga kowanne matashi da ke kasar

- Sarkin ya bayyana cewa bijirewa hakan zai saka mutum ya tafi gidan yari

- Ya bayyana cewa gwamnati ta yi alkawarin siyawa mutum gida da kuma daukar nauyin bikin auren

Sarkin Swaziland Mai Martaba Mswati III, ya bayyana cewa daga watan Yuni 2019 maza zasu fara auren mata sama da daya a kasar ko kuma su tafi gidan yari idan suka bijirewa umarnin sa.

Sarkin, wanda ya ke da mata 15 da 'ya'ya guda 25, yayin da mahaifinsa wanda ya gaje shi yake da mata sama da guda 70 da kuma 'ya'ya sama da 150, ya bayyana cewa mata sun ninka maza yawa a kasar Swaziland sosai, inda ya bayyana hakan a matsayin babbar matsala ga kasar.

Garin dadi ba kusa ba: Wani sarki ya saka doka akan mazajen kasarsa da su dinga auren mata a kalla guda hudu

Garin dadi ba kusa ba: Wani sarki ya saka doka akan mazajen kasarsa da su dinga auren mata a kalla guda hudu
Source: Facebook

A cewar IHarare, mazajen kasar Swaziland an bukaci su auri mata fiye da daya, koda hakan zai bai wa kowacce mace samun miji a kasar.

A wata sanarwa da ya fitar, Mai Martaba Mswati ya yi kira ga daukacin mazan kasar da su auri mata akalla guda biyar, inda ya bayyana cewa ya yi alkawarin gwamnati za ta dauki nauyin duk wani wanda zai auren, ta hanyar siya masa gida kuma ta dauki nauyin hidimar bikin.

KU KARANTA: 'Yar gidan Sarkin Kano ta mayarwa da Ganduje raddi

Sarkin ya yi gargadin cewa duk wani wanda ya ki bin umarnin sa, zai fuskanci daurin rai da rai a gidan yari.

Ana ta samun yawaitar mata a duniya, masana sun nuna cewa za a kai wani lokaci da maza zasu yi karanci a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa nan: Domin karuwa cikin wannan wata mai alfarma na Ramadana

Source: Legit

Mailfire view pixel