Buhari ya yi ma wata kyakkyawar budurwa mai shekaru 27 nadin mukami mai muhimmanci

Buhari ya yi ma wata kyakkyawar budurwa mai shekaru 27 nadin mukami mai muhimmanci

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada wata budurwa mai shekaru 27, Hannatu Muhammad mukami a majalisar gudanarwa ta hukumar yaki da rashawa da makamantan laifuka, watau ICPC, sai dai hakan ya bar baya da kura.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan Najeriya da dama sun yi cece kuce tare da musayar ra’ayi game da nadin da shugaba Buhari yayi ma Hannatu, inda wasu ke ganin bata da wani cikakken kwarewa a kowanne fanni, don haka menene dalilin da yasa Buhari ya nadata wannan mukami.

Buhari ya yi ma wata kyakkyawar budurwa mai shekaru 27 nadin mukami mai muhimmanci
Hannatu
Asali: UGC

KU KARANTA; Mai martaba Sarkin Bichi ya yi fatali da maganan samun baraka tsakaninsa da Sarkin Kano

Ita dai Hannatu an haifetane a ranar 20 ga watan Maris na shekarar 1992, kuma tayi makarantar Firamari a Essence Kaduna daga shekarar 1995 – 2001, sai ta koma makarantar sakandari ta El-Ameen dake Minna daga shekarar 2001 zuwa 2008 don karatun sakandari.

Buhari ya yi ma wata kyakkyawar budurwa mai shekaru 27 nadin mukami mai muhimmanci
Yayin nadinsu
Asali: UGC

Hannatu ta kammala karatun digiri a fannin kimiyyar hada magunguna a jami’ar Ahmadu Bello a shekarar 2014, sa’annan yanzu haka tana karatun Masters a ilimin tafiyar da kasuwanci a ABU, sai dai bata taba yin kwakkwaran aiki a gwamnatance ba, wanda hakan yasa wasu ke ganin rashin dacewarta.

Ta yi aikin samun horo da sanin makaman aiki a matsayin dalibar jami’a a shagon magani na H-Medix, tayi aikin wucin gadi a hukumar kula da magungun da abinci na NAFDAC, tayi bautan kasa a asibitin INEC, sai kuma tayi aiki da kamfanin hada magunguna na Green Forest daga 2017 zuwa 2018.

Sai dai ana tunanin shugaba Buhari yayi amfani da sashi na (f) na dokokin ICPC ne wajen nada Hannatu, wanda ya bukaci a nada matashi da bai gaza shekara 21 kuma bai haura shekara 30 ba a majalisar gudanarwar hukumar, amma sashin bai yi magana game da kwarewar wanda za’a nada ba.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel