Ban karbi wani umurni daga kotu kan nada sabbin sarakuna ba - Kwamishinan shari'ah na Kano

Ban karbi wani umurni daga kotu kan nada sabbin sarakuna ba - Kwamishinan shari'ah na Kano

Kwamishinan shari'ah na jihar Kano, Barista Ibrahim Mukhtari ya fada wa BBC cewa har zuwa daren ranar Juma'a, bai karbi wani umarni daga kotu (game da batun nada sabbin sarakuna da kirkirar karin masarautu na gwamnatin Kano) ba.

A daidai lokacin da labarin dakatar da gwamnatin jihar Kano da kotu tayi daga kafa sabbin masarautu a jihar Kano, kwamishinan shari’ah na jihar, Barista Ibrahim Mukhtari ya bayyana cewa har zuwa daren ranar Juma’a, 10 ga watan Mayu, bai amshi wani umurni daga koyu akan lamarin nadin sabbin saranan ba.

Da farko dai an rahoto cewa wata babbar kotun jihar Kano, ta dakatar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje daga kafa sabbin masarautu hudu da majalisar dokokin jihar ta yi.

Ban karbi wani umurni daga kotu kan nada sabbin sarakuna ba - Kwamishinan shari'ah na Kano
Ban karbi wani umurni daga kotu kan nada sabbin sarakuna ba - Kwamishinan shari'ah na Kano
Asali: Twitter

Wadannan masarautu sun hada da Bichi, Gaya, Rano da Karaye. Dakatarwar da kotu tayi ya biyo bayan wani kara da wasu yan majalisa suka shigar gabanta inda suke kalubalantar matakin dokar.

An tattaro inda Kwamishinan ke fadin cewa: "Ban san da kara ba, kawai dai yadda kuke ji a gari, (ni ma) haka nake ji a gari. Ni ban ga oda ta kotu ba kowacce iri."

Ya kara da cewa don haka ba za su ce komai a kai ba, har sai sun ga takardar kotu.

Za dai a zuba ido a gani ko gwamnatin jihar Kano za ta dakatar da nadin sarakunan a ranar Asabar kamar yadda ta tsara bisa umarnin kotu, ko kuma za ta yi biris da umarnin ta ci gaba da shagulgulan bai wa sabbin sarakunan hudu sandunan girma.

KU KARANTA KUMA: Shugaban masu rinjaye na majalisar dokoki ya fadi fa'idar kirkiran sabbin masarautu a Kano

Sarakunan dai sun hadar da Alhaji Aminu Ado Bayero, zai jagoranci masarautar Bichi, da Dr. Ibrahim Abubakar a matsayin sarkin Karaye sai Tafida Abubakar Ila sarkin Rano da kuma Alhaji Ibrahim Abdulkadir a matsayin sarkin Gaya.

'Yan majalisar bangaren jam'iyyar PDP mai adawa wadanda marasa rinjaye ne suka shigar da karar bisa jagorancin shugabansu Rabiu Sale Gwarzo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Ku latsa domin karuwa cikin wannan wata mai albarka na Ramadana: https://fb.gg/play/ramadan_ramadan

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel