Sheikh Daurawa, Abba Koki da Kandahar sun yi murabus daga gwamnatin Ganduje

Sheikh Daurawa, Abba Koki da Kandahar sun yi murabus daga gwamnatin Ganduje

Akalla malaman addinin Musulunci hudu ne suka sanar da murabus dinsu daga gwamnatin Gwamna Abdullahi Ganduje a jihar Kano.

Malaman da suka yi murabus sun hada da Kwamanda Janar na hukumar Hisbah, Aminu Daurawa; Shugaban hukumar mahajatta na jihar Kano, Abba Koki; Kwamishinan hukumar gudanar da Shari’a na I, Ababukar Kandahar da kuma Kwamishinan hukumar Zakkah da Hubsi na II, Nazifi Inuwa.

Dukkanin malaman guda hudu sun gabatar da wasikun ajiye aiki ne a ranar 9 ga watan Mayu, 2019.

Sheikh Daurawa, wanda ya kasance daya daga cikin yan tsirarun malamai da suka yi Allah wadai da bidiyon cin hancin gwamnan a hudubarsa na ranar Juma’a, yace ya yi murabus ne akan wasu dalilai na kansa.

Sheikh Daurawa, Abba Koki da Kandahar sun yi murabus daga gwamnatin Ganduje
Sheikh Daurawa, Abba Koki da Kandahar sun yi murabus daga gwamnatin Ganduje
Asali: UGC

“Mun ajiye aiki ne akan wasu dalilai na kanmu," Sheikh Daurawa, Kandahar da Inuwa suka bayyana a wasikunsu, inda suka bayyana wasu dalilai na kansu da ya saba ma bukatar ofishinsu.

KU KARANTA KUMA: Samar da sabbin masarautu 4: Al’umman Kano sun yi zanga-zanga

Amma Mallam Koki bayyana dalilin lafiya da wasu ayyukan kansa a matsayin dalilinsa na murabus.

A makon da ya gabata ne, gwamnan ya yi hannunka mai sanda ga Mallam Daurawa akan rashawa, inda ya bayyana cewa zai yi garambawul a hukumar Hisbah don aiki mai inganci.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel