Ku sadu da Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele

Ku sadu da Gwamnan babban bankin Najeriya, Godwin Emefiele

Cikin wannan rahoto za mu kawo muku wasu takaitattun ababe da suka shafi rayuwar Godwin Emefiele, gwamnan babban bankin Najeriya da shugaban kasa kasa Muhammadu Buhari ya sake lamuncewa wajen tsawaita wa'adin mukamin sa a karo na biyu.

A halin yanzu Emefiele ya kasance Gwamnan babban bankin kasar nan bayan ya kasance shugaban bankin Zenith gabanin nadin mukamin sa a shekarar 2014 a gwamnatin tsohon shugaban kasa, Goodluck Jonathan.

Yayin da tsatson sa ya kasance karamar hukumar Ika ta Kudu a jihar Delta, an haife shi a ranar 4 ga watan Agustan 1961 a jihar Legas inda ya kammala karatun firamare cikin yankn Victoria Island da kuma Igbosere a shekarar 1973.

Godwin Emefiele
Godwin Emefiele
Asali: UGC

Ya kammala karatun sa na Sakandire tare da samun takardar shaidar jarrabawar hukumar WAEC a shekarar 1978 cikin birnin Ikeja a jihar Legas.

Ya kammala karatun digiri na farko da na biyu a fannin harkokin kudi da kasuwanci a jami'ar Najeriya cikin shekarar 1984 da kuma 1986.

Ya yi wasu karatuttuka daban daban musamman a fannin tsimi da tanadi a jami'ar Oxford, jam'iar Stanford, Havard, da kuma jam'iar Pennsyvania da ke kasar Amurka.

Bayan samun kwarewa a kan sana'ar aikin banki ta fiye da tsawon shekaru 18, Godwin ya rike matakai daban daban a bankin Zenith gabanin kasancewar mai rike da akalar jagoranci ta babban bankin kasar nan.

KARANTA KUMA: APC da INEC na neman kashe ni a siyasance - Okorocha

Mahaifiyar sa ta riga mu gidan gaskiya a watan Afrilun 2016 inda aka gudanar da jana'izar ta bisa ga tanadi da kuma al'adu na mabiya addinin Kirista.

A halin yana nan zaune lafiya cikin farin ciki tare da ma dakin sa Margaret Emefiele da kuma 'ya'yan sa guda biyu reras.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.android&pid

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel