Yanzu Yanzu: An tsige kakakin majalisar Jigawa

Yanzu Yanzu: An tsige kakakin majalisar Jigawa

- An tsige kakakin majalisar dokokin jihar Jigawa, Isah Idriz Gwaram

- Yan majalisa a jihar suka tsige Gwaram a lokacin wani zama a ranar Alhamis, 9 ga watan Mayu

- An maye gurbinsa da Idris Garba Kareka, wanda ya kasance tsohon kakakin majalisar

Rahotanni da ke zuwa mana sun nuna cewa, an tsige kakakin majalisar dokokin jha Jigawa, Hon. Isah Idris Gwaram.

An tsige shi ne a safiyar yau Alhamis, 9 ga watan Mayu lokacin wani zama.

Yanzu Yanzu: An tsige kakakin majalisar Jigawa

Yanzu Yanzu: An tsige kakakin majalisar Jigawa
Source: UGC

Yan majalisa sun zabi tsohon kakakin majalisa, wanda aka tsige a 2017, Hon. Idris Garba Kareka domin ya maye gurbinsa.

KU KARANTA KUMA: Ra'ayoyin jama'a akan kacaccala masarautar kano zuwa yanka 5 da gwamnatin Ganduje tayi

A halin da ake ciki, Legit.ng ta rahoto a baya cewa don guje ma shirin tsige gwamnan jihar Adamawa mai barin gado, Mohammed Umaru Jibrilla Bindow, da kakakin majalisar dokokin jihar, anyi gaggawan ficewa da sandar ikon majalisa daga harabar majalisar dokokin a ranar Talata, 3 ga watan Afrilu.

Bayan tafiya hutu na kimanin wata guda, majalisar ta dawo zama a ranar Talata domin duba wasikar yan majalisa daga gwamnan, cewa ya tafi hutun makonni biyu.

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Source: Legit

Mailfire view pixel