Ina sane da nauyin dake kaina, kuma ina sane da abinda nake yi sarai – Shugaba Buhari

Ina sane da nauyin dake kaina, kuma ina sane da abinda nake yi sarai – Shugaba Buhari

Shugaban kasa Muhammadu Buhari ya tabbatar ma yan Najeriya cewa ba zai basu kunya ba a wa’adin mulkinsa na biyu, inda ya kara da cewa yana sane sarai da halin da ake ciki, yana sane da irin nauyin dake rataye a wuyansa, kuma ya san matakin daya kamata ya dauka.

Buhari ya bayyana haka ne bayan kammala sauraron tafsirin Al-Qur’ani mai girma daya gudana a babban masallacin fadar shugaban kasa dake Aso Rock Villa, inda yace ya sani cewa ba karamin nauyi bane a wuyansa, kuma zai cigaba da yin duk mai yiwuwa don ingantan rayuwar dan Najeriya.

KU KARANTA: Karamar magana ta zama babba: Batun raba masarautar Kano gida 4 ta samu tagomashi

Ina sane da nauyin dake kaina, kuma ina sane da abinda nake yi sarai – Shugaba Buhari
Buhari yana sauraron Tafsir
Asali: Facebook

“Na san bukatun yan Najeriya, da kuma irin rawar da suke bukata na taka, kuma zan cika musu dukkanin burace buracensu, ba zan basu kunya ba, zan cigaba da yin iya bakin kokarina don ganin na faranta musu.” Inji shi.

Daga karshe Buhari yayi kira ga yan Najeriya dasu kasance masu bin doka da oda wajen tafiyar da rayuwarsu, sa’annan ya shawarcesu dasu yi amfani da damar Azumin watan Ramadana don samar da zaman lafiya a kasar.

Shima a nasa jawabin, babban limamin fadar shugaban kasa, Sheikh Abdulwaheed Sulaiman ya bayyana godiyarsa ga Allah madaukakin Sarki da Yasa aka gudanar da zaben 2019 cikin kwanciyar hankali da lumana, sa’annan yayi kira ga Musulmai dasu kasance masu yawan neman gafara a wannan wata.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel