Tirkashi: Sarkin Katsina ya bai wa Ministoci sako su kaiwa shugaba Buhari

Tirkashi: Sarkin Katsina ya bai wa Ministoci sako su kaiwa shugaba Buhari

- Ran Sarkin Katsina ya baci akan matsalar tsaro a jihar, inda ya aikawa da shugaba Buhari wani muhimmin sako

- Ya bukaci Ministocin shugaba Buharin da su sanar da shi cewa suna bukatar a kawo karshen matsalar tsaro a Najeriya

Jiya Litinin ne 6 ga watan Mayu, 2019, Sarkin Katsina Mai Girma Abdulmumini Kabir Usman ya bukaci ministan noma Audu Ogbeh da ya sanar da shugaban kasa Muhammadu Buhari cewa manoma da makiyaya na jihar Katsina, sun bar gonakin su da dabbobin su saboda tsoron masu garkuwa da mutane.

Ministan da gwamnan babban bankin Najeriya Godwin Emefiele sun ziyarci fadar Sarkin Katsinan, inda suka je domin gabatar da irin auduga da kayan noma ga manoman jihar Katsina.

Tirkashi: Sarkin Katsina ya bai wa Ministoci sako su kaiwa shugaba Buhari
Tirkashi: Sarkin Katsina ya bai wa Ministoci sako su kaiwa shugaba Buhari
Asali: Facebook

"Ina so ku sanar da shugaban kasa cewa ya kamata mu lura da kanmu sosai, sannan kuma mu kare lafiyar mutanen mu. Saboda duk wannan shirye-shiryen da ake kawowa ba za su taba aiki ba har sai an tabbatar da cewa an magance tsaro a kasar nan," in ji Sarkin.

"Kullum sai na samu rahoto daga wajen Hakimai da masu gari da ke nuna cewa an sace mutane ko an kashe," Sarkin ya kara da cewa, ya na zargin wasu manyan kasar nan, 'yan siyasa da masu kudi da hannu a cikin wannan kashe-kashen da ke faruwa a kasar nan.

KU KARANTA: Satar mutane ita ce sabuwar sana'ar matasan Najeriya - Buhari

"Wace irin riba zaku samu da kashe mutane da kuke sawa ana yi, ana sace mutane? Abin babu dadin ji ko kadan. Ban taba ganin kasa irin wannan ba; muna zama kamar na dabbobi. Kwanaki uku da suka wuce an sace Magajin Garin Daura, babu wani wanda ya tsira a wannan lokacin, ko a gida ko a hanya," in ji shi.

Majiyarmu LEGIT.NG ta kawo muku rahoton cewa yankuna da yawa a jihar Katsina, musamman ma yankunan da suka hada iyaka da jihar Zamfara, suna fama da matsalar tsaro.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel