Wata babbar mota ta fadi a jihar Kaduna ta yi sanadiyyar rayukan mutane da dama

Wata babbar mota ta fadi a jihar Kaduna ta yi sanadiyyar rayukan mutane da dama

- Wata katuwar tirela da ta dauko shanu da mutane ta fadi a kan hanyar Abuja zuwa Kaduna, inda ta yi sanadiyyar mutuwar mutane masu yawan gaske kuma ta kashe shanun da ta dakko da yawa

- Tirelar ta fadi ne akan gadar Azara da ke karamar hukumar Kagarko cikin jihar Kaduna

Mutane masu yawan gaske sun rasa rayukan su sanadiyyar wata babbar mota da ta fadi akan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

Rahotanni sun nu na cewa babbar motar ta fadi ne a lokacin da motar ta kwace daga hannun direban akan babbar hanyar.

Direban ya ciko motar da shanu ne da kuma mutane da yawa a saman motar, yayin da motar ta kwace daga hannun shi.

Wata babbar mota ta fadi a jihar Kaduna ta yi sanadiyyar rayukan mutane da dama

Wata babbar mota ta fadi a jihar Kaduna ta yi sanadiyyar rayukan mutane da dama
Source: Facebook

An ce motar ta fadi ne a dai dai kan gadar Azara da ke karamar hukumar Kagarko cikin jihar Kaduna.

Wannan labari ya na zuwa ne bayan irin harin da 'yan bindiga su ke kai wa yankunan, musamman ma kan babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

KU KARANTA: Kasashe 10 da suke biyan albashi mafi karanci a 2019

Ana ta samun yawan hadarurruka a kan manyan hanyoyin kasar nan, duk kuwa da irin kokarin da hukumar yaki da hadura ta kasa ta ke yi wurin ganin an rage asarar rayuka a fadin kasar.

Hukumar ta sha yin gargadi ga direbobi musamman na manyan mota akan su lura kuma su dai na yawan gudu akan manyan tituna musamman ma idan sun dauko kaya a cikin motocin su.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Mailfire view pixel