Gagga gaggan barayi sun yi awon gaba da mutane 3, sun kashe 4 a Neja

Gagga gaggan barayi sun yi awon gaba da mutane 3, sun kashe 4 a Neja

Wasu gungun yan bindiga dauke da muggan makamai sun kai mummunan farmaki a wani kauye mai suna Madaka dake cikin karamar hukumar Rafi ta jahar Neja inda suka bindige mutane hudu har lahira, tare da yin garkuwa da wasu mutane uku.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito yan bindigan sun fara yada zango ne a wani ruga dake kusa da kauyan Madaka inda suka ajiye baburansu, daga nan suka sadado zuwa kauyen har suka aikata ma mazauna kauyen wannan ta’asa.

KU KARANTA: Sabon salo: Buhari yayi sabbin nade nade guda 26 daga Landan

Kauyen Madaka yayi kaurin suna wajen fama da hare haren yan bindiga, sakamakon yan bindiga, barayi, yan fashi, da masu garkuwa da mutane sun mayar da dazukan dake zagaye da kauyen mafakarsu da sansaninsu.

Dakacin kauyen Madaka, Zakari Ya’u ya bayyana cewa mamayansu yan bindigan suka yi, kuma suka aikak musu danyen aiki cikin kankanin lokaci ba tare da sun samu damar kare kansu ba, kuma ko kafin su ankara har sun tsere.

Shugaban riko na karamar Rafi, Bala Bawa ya tabbatar da aukuwar lamarin, inda yace yan bindigan sun dira kauyen ne dauke da muggan makamai na zamani, sa’annan ya kara da cewa sun tafi da mutane uku.

Ko a watan Disambar bara, sai da yan bindiga suka kashe wasu jami’an rundunar Sojan kasa guda biyu a wani harin kwantan bauna da suka dana musu a yayin da suka yi kokarin kai ma al’ummar kauyen Madaka dauki bayan samun rahoton harin yan bindiga a kauyen.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit Nigeria

Mailfire view pixel