Tsaro: Buhari ya amince da kafa 'yan sandan unguwanni - IG

Tsaro: Buhari ya amince da kafa 'yan sandan unguwanni - IG

Shugban kasa Muhammadu Buhari ya amince da kafa 'yan sandan unguwanni a matsayin wata mataki na magance karuwar barazanar tsaro da ake kara samu a sassan Najeriya a cewar Sufeta Janar na 'yan sandan Najeriya.

Sufeta Janar na 'yan sanda, Mohammed Adamu ya bayar da wannan sanarwar ne a ranar Talata a wurin taron Shugabanin Gargajiya na Arewa da aka gudanar a Kaduna.

Mahalarta taron sun tattauna muhimman batutuwa ne da suka shafi tsaro musamman a Arewacin kasar.

Premium Times ta ruwaito cewa mataimakin shugban kasa, Farfesa Yemi Osinbajo ya ce gwamnatin tarayya za ta fitar da sabuwar tsari na 'yan sandan unguwanni domin inganta harkokin tsaro.

Tsaro: Buhari ya amince da kafa 'yan sandan unguwanni - IG
Tsaro: Buhari ya amince da kafa 'yan sandan unguwanni - IG
Asali: UGC

DUBA WANNAN: Tsallake rijiya da baya: Abubuwa 5 da ya kamata ku sani a kan Zainab Aliyu

Osinbajo ya ce wannan za ta zama shimfida ga sabuwar tsarin aikin 'yan sanda a Najeriya.

Ya bayar da tabbacin cewa kafa 'yan sandan unguwani ba zai rage wa jami'an rundunar 'yan sandan Najeriya ikon su ba.

A jawabin da ya yi a wurin taron a Kaduna, Sufeta Janar na 'yan sandan ya ce rundunar ta samu nasarori masu yawa wurin kare afkuwar laifuka da barazana ga rayuka da dukiyoyin al'umma a kwanakin nan.

Mr Adamu ya ce an kara samun nasarorin sosai tun bayan kaddamar da atisayen 'Operation Puff Adder'.

"Sabon tsarin 'yan sandan unguwani zai inganta samar da tsaro a tsakanin al'umma tare da magance barazana ga tsaro," inji shi.

IG din ya ce Najeriya ta kwakwayo wannan tsari ne daga kasar Ingila inda ake amfani dashi domin inganta tsaro.

Za a tsara shirin yadda zai dace da irin hanyoyin samar tsaro na gargajiya ya ke a Arewacin Najeriya.

"Za a zabo jami'an tsaron ne daga cikin mazauna unguwani domin su bayar da gudunmawa inda za suyi aiki karkashin rundunar 'yan sandan Najeriya.

"Za a kaddamar da wannan sabuwar tsarin ne bisa umurnin shugaban kasa, Muhammadu Buhari, babban kwamandan hafsoshin Najeriya" inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu :https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel