A rina: Ana biyan Sojan Najeriya N1000, ana biyan dan Boko Haram $3000 a duk rana

A rina: Ana biyan Sojan Najeriya N1000, ana biyan dan Boko Haram $3000 a duk rana

Kwamitin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya kafa don magance matsalolin da yan gudun hijira suke fuskanta a yankin Arewa maso gabas ta bayyana bukatar kula da walwalar dakarun Sojin Najeriya, musamman wadanda suke bakin daga, duba da cewa mayakan Boko Haram sun fisu albashi.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Dakta Sidi Ali Muhammed guda daga cikin yayan kwamitin ne ya bayyana haka, inda yace kungiyar Boko Haram na biyan duk mayakinta karancin albashin dala dubu uku ($3000), kimanin naira miliyan daya da dubu dari takwas (1,080,000) kenan a duk rana.

KU KARANTA: Ke duniya: Matashi ya kashe mahaifinsa, ya babbaka gawarsa

Sidi ya bayyana haka ne a yayin taron kaddamar da rahoton bankin lamuni na duniya, IMF, game da tattalin arzikin kasashen nahiyar Afirka daya gudana a Abuja a ranar Litinin, 29 ga watan Afrilu, inda yace amma Sojan Najeriya dubu daya (1000) ake biyansa a duk rana.

Sidi ya kara da cewa akwai masu daukan yakin da Boko Haram take yi da Najeriya, “Bari na baku misali, Sojan Najeriya dake yaki a Arewa maso gabasa yana samun N1,000 ne a kowanne rana a matsayin alawus, yayin da Sojan Boko Haram ke samun $3,000 a kowanne rana.

“A wasu lokuttan ma kai tsaye za’a biyaka kudinka a matsayinka na dan ta’adda kafin ku tafi kai hari, don haka ya zama wajibi mu dauki mataki akan yadda Boko Haram take daukan matasanmu a matsayin Sojonta.” Inji shi.

Sai dai Sidi yace akwai bukatar duba yiwuwar yafiya da afuwa ga yan ta’adda idan har anaso a kawo karshen yaki da Boko Haram. “Idan har yafiya da afuwa zai kawo zaman lafiya a yankin, ya kamata mu duba yiwuwar yin hakan.

“Mafi muhimmanci shine mu rage yawan matasa marasa aikin yi dake gararamba akan titunanmu don hana Boko Haram samun daman daukansu aiki, ana kashe Boko Haram a kullum, amma suna daukan sabbin mayaka a kullum saboda akwai riba sosai a aikin.” Inji shi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel