Gwamnatin tarayya ta bayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu ga ma'aikata

Gwamnatin tarayya ta bayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu ga ma'aikata

- A jiya ne gwamnatin tarayya ta bayar da sanarwar bai wa ma'aikata hutun kwana daya domin basu damar gabatar da bikin murnar ranar su ta ma'aikata

- Ma'aikatan za su gabatar da hutun na su a gobe Laraba, inda za su cigaba da aiki ranar Alhamis

Gwamnatin tarayya ta bayyana gobe Laraba 1 ga watan Mayu, 2019, a matsayin ranar ma'aikata.

Ministan harkokin cikin gida, Abdulrahman Dambazau, shine ya bayyana hakan, a madadin gwamnatin tarayya a wata sanarwa da babban sakataren ma'aikatar Barista Georgina Ekeoma Ehuriah, ya sanyawa hannu jiya Litinin, 29 ga watan Afrilu, 2019.

Gwamnatin tarayya ta bayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu ga ma'aikata

Gwamnatin tarayya ta bayyana gobe Laraba a matsayin ranar hutu ga ma'aikata
Source: Depositphotos

Ya taya dukkanin ma'aikatan Najeriya murna akan irin ayyukan da suke gabatarwa da kuma irin sadaukar da kansu wurin ganin sunyi aiki tukuru domin cigaban kasarmu Najeriya.

Har ila yau Dambazau ya yabawa ma'aikatan akan tabbatar da manufofin gwamnatin tarayya na ayyukan kasar nan, sannan ya yabawa kasashen waje da irin kokarin da suke wurin ganin sun kawo ayyukan cigaba a fadin kasar.

KU KARANTA: Kasashe biyar da suka fi ko ina jin dadin rayuwa, da kasashe biyar da suka fi ko ina kuncin rayuwa

Idan ba a manta ba makonni kadan da suka gabata shugaban kasa Muhammadu Buhari ya sanya hannu akan dokar karawa ma'aikata albashi a kasar nan, inda ya mayar da karancin albashi zuwa naira dubu talatin daga naira dubu sha takwas da ake biya a da.

Sai dai kuma wani hanzari ba gudu ba, da yawa daga cikin gwamnonin Najeriya sun bayyana cewa gaskiya baza su iya biyan sabon albashin da gwamnatin tarayyar ta mayar doka ba, inda har wasu masu hasashe a kasar suke ganin karin albashin zai iya kawo rikici a fadin kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit Newspaper

Mailfire view pixel