Direba ya kashe matar maigidanshi, saboda ya kore shi a aiki

Direba ya kashe matar maigidanshi, saboda ya kore shi a aiki

- Hukumar 'yan sanda ta cafke wani direba da ya kashe matar ubangidansa, saboda maigidan nasa ya kore shi a aiki

- Mutumin ya bayyana cewa ya aika laifin ne saboda ya rama abinda ubangidan nashi ya yi masa

Wani direba dan shekaru 37, mai suna Morenikeji Adeyemi ya bayyana cewa shi ne ya kashe matar ubangidansa. Adeyemi ya bayyana hakan a lokacin da ake bincikarshi a ofishin 'yan sanda na jihar Oyo.

Kwamishinan 'yan sanda na jihar Oyo, Shina Olukalu, ya ce sun kama wanda ake zargin a Sango Ota da ke jihar Ogun, garin da ya koma bayan ya aikata laifin nashi.

Direba ya kashe matar maigidanshi, saboda ya kore shi a aiki

Direba ya kashe matar maigidanshi, saboda ya kore shi a aiki
Source: Facebook

A lokacin da yake bayani, Adeyemi ya ce:

"Ban ji dadi ba lokacin da maigidana ya kore ni a aiki, A dai dai lokacin matata ta haihu, saboda rashin kudin magani ya sa jaririn ya mutu."

KU KARANTA: Kashe - kashe: An bukaci a sanya dokar ta baci a jihohin Zamfara, Katsina da Kaduna

"Don haka, na yanke shawarar nima na je na rama. Matar maigidan nawa ta taba yi mini maganar cewa tana fama da matsalar aljanu, kuma na yi mata alkawarin zan kai ta wurin da za ayi mata addu'a a bata magani.

"Sai na yi amfani da wannan damar na kirata na ce ta zo muje wurin mai maganin, muka fita a motarta, akan hanyar mu sai ta ce za ta zaga ta dawo, sai na tsaya ta sauka ta shiga cikin daji, sai na bita cikin dajin na jata cikin ruwa har sai da ta mutu. Sai na dauki motar ta na gudu."

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit.ng

Mailfire view pixel