An yi tuya an mance da albasa: Babu hukumar soji a sabon karin albashi da aka gabatar

An yi tuya an mance da albasa: Babu hukumar soji a sabon karin albashi da aka gabatar

- Hukumar sojin Najeriya ta karyata wata jita jita da ake yadawa aa kafar sadarwa ta zamani da ke nuna cewa an karawa ma'aikatan hukumar albashi wanda zai fara aiki a watan Mayu da zamu shiga

- Hukumar ta karyata wannan jita-jita ta ce bata da tushe bare makama

Jiya Juma'a ne 26 ga watan Afrilu, hedkwatar hukumar soji ta kasa ta ce sabon karin albashin ma'aikata da gwamnatin tarayya ta kaddamar ba ta hada da ma'aikatan hukumar sojin kasar nan ba.

Hukumar ta mayar da martani ne ga wasu takardu na karya da suke yawo a kafar sadarwa na zamani akan wannan batu.

"Saboda haka, hukumar ta na so ta bayyana wa al'umma cewa wannan takardu na karya ne ba su da tushe, kuma ba su fito daga wurin hukumar soji ba, kuma ana yada su ne domin a kawo rudani ga jami'an hukumar soji na kasar nan, saboda babu hukumar soji a karin albashin da aka yi," in ji Col. Onyema Nwachukwu.

An yi tuya an mance da albasa: Babu hukumar soji a sabon karin albashi da aka gabatar
An yi tuya an mance da albasa: Babu hukumar soji a sabon karin albashi da aka gabatar
Asali: UGC

Nwachukwu ya ce hukumar ba ta ji dadin ganin takardun karyar da suke yawo a kafar sada zumunta ba, da ke nuna sabon tsarin albashin ma'aikata, wanda zai fara aiki a watan Mayun 2019.

"Hukumar ta na sanar da jama'a cewa wannan takardu babu su, kuma ba daga hukumar soji suka fito ba.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An sace wasu 'yan China a Najeriya

"Idan ba a mance ba shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya sanya hannu akan dokar karin albashin ma'aikata, inda za a dinga biyansu naira dubu 30 a kowanne wata.

"Ya na da matukar muhimmanci mutane su gane cewa hukumar soji ba ta karawa ma'aikatan ta albashi ba," in ji Nwachukwu.

Saboda haka ya bukaci ma'aikata hukumar soji da al'umma su yi watsi da wannan takardu na karya da ake yadawa a kafar sadarwa na zamani.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel