Atiku jikanmu ne, jininmu ne – Inji babbar masarautar jahar Jigawa

Atiku jikanmu ne, jininmu ne – Inji babbar masarautar jahar Jigawa

Wani basarake daga masarautar Dutse ta jahar Jigawa ya tabbatar da ikirarin da tsohon dan takarar shugaban kasa a jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku Abubakar yayi na cewa mahaifiyarsa yar jahar Jigawa ce, inda bada tabbacin lallai mahaifiyar Atikun diyarsu ce, Atiku kuma jikansu ne.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito wannan basaraken da baya bukatar a bayyana sunansa ko sarautarsa ya bayyana cewa mahaifiyar Atiku diyace ga marigayi Malam Abdullahi dan asalin Jigawar Sarki ta jahar Jigawa.

KU KARANTA: Manyan jiragen ruwa 28 zasu sauke man fetir da kayan masarufi a tashoshin Legas

Atiku jikanmu ne, jininmu ne – Inji babbar masarautar jahar Jigawa
Atiku
Asali: Twitter

Basaraken yace dalilinsa na boye kansa shine sakamakon yadda aka siyasantar da batun tushen Atikun, don haka bayaso ya shiga cikin cece kuce ko kuma sabanin yan siyasa, musamman duba da matsayinsa na mai rike da sarauta.

“Ina tabbatar muku da cewa mahaifiyar Atiku, marigayiya Kande, yar asalin garin Dutse ce, kawunta kuma, Adamu Ma’aruf, shine babban limamin Masallacin garin Dutse har lokacin daya rasu shekaueu 5 bayan kafa jahar Jigawa.” Inji shi

Shima wani mazaunin Dutse mai shekaru 100 a duniya, Malam Isiyaku Adamu ya bayyana cewa suna kiran mahaifiyar Atiku da suna ‘Kande yar Malam’ kumata auri mahaifin Atiku Malam Garba, wanda ya fito daga Sakkwato.

“A gidanmu Malam Garba ya sauka, ana kiran gidan ‘gidan Malamai’, ya aureta ya kaita Adamawa inda aka haifi Atiku, Kande kanwar Alhaji Ali da Azumi ce, don haka Kande diyarmu ce, kuma Atiku jikanmu ne, dukkanmu Fulani ne, kakanninmu Malamai ne, shi yasa ake kiran gidanmu gidan Malamai.” Inji shi

Idan za’a tuna jam’iyyar APC ce ta fara shaida ma kotun sauraron korafin zaben shugaban kasa cewa Atiku Abubakar bad an Najeriya bane, dan asalin kasar Kamaru ne, don haka bashi da hurumin tsayawa takarar shugabancin kasar Najeriya.

Sai dai Atikun ya mayar dsa martani, inda yace a ranar 25 ga watan Nuwambar 1946 aka haifeshi a kauyen Jada dake cikin jahar Adamawa, wanda a wancan zamani tana karkashin lardin Arewacin kasar Kamaru ne.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel