Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Yan bindiga sun yi awon gaba da Matan aure 9 a jahar Neja

Innalillahi wa Inna Ilaihi raji’un: Yan bindiga sun yi awon gaba da Matan aure 9 a jahar Neja

Gungun wasu miyagu yan bindiga marasa Imani sun yi awon gaba da wasu matan aure guda Tara da tsakar rana a kauyen Kuchi dake cikin karamar hukumar Munya ta jahar Neja a ranar Litinin, 22 ga watan Afrilu.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito a kokarinsu na yin garkuwa da matan auren, yan bindigan sun dirka ma wasu mutane uku bindiga, wanda hakan yayi sanadiyyar mutuwar guda daga cikinsu, yayin da sauran biyun suka samu rauni.

KU KARANTA: Rashin iya mulki: Dan majalisa ya nemi gwamnan jigawa yayi murabus daga kujerarsa

Wani majiya mazaunin kauyen da lamarin ya faru a gabansa, Salisu Garba ya bayyana cewa daga cikin Mata Tara da yan bindigan suka tattara, akwai guda biyar masu shayarwa, sai kuma guda biyu masu matsakaicin shekaru.

Malam Salisu ya kara da cewa da duka matan auren suna da alaka da mutumin da yan bindigan suka kashe, dukkansu yan uwan juna ne ta jini da kuma ra auratayya.

Mukaddashin shugaban karamar hukumar Munya, Joshua Musa ya tabbatar da aukuwar wannan lamari mai muni, inda yace tuni jami’an tsaro sun bazama farautar yan bindigan tare da ganin sun ceto matan gaba dayansu.

Sai dai Mista Joshua ya tabbatar da cewa yan bindigan sun nemi iyalan Matan, kuma sun nemi har sai an biyasu kudin fansa naira miliyan dari takwas (N800,000,000) kafin su sakesu.

Ba wannan bane karo na farko da ake samun garkuwa da mutane a yankin Munya ba, inda ko a bara sai da rundunar Soja ta 3 ta tura dakarunta suka yi sansani a kauyukan Fukka, Kubarachi, Zazzaga dajin Kabulla don magance hare haren yan bindiga a yankin.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit.ng

Online view pixel