Tun da aka ci zabe, Gwamnati tayi shiru da batun karin albashi – Shehu Sani

Tun da aka ci zabe, Gwamnati tayi shiru da batun karin albashi – Shehu Sani

- Shehu Sani yayi magana a game da batun karin albashi

- Sanatan yace an yi watsi da maganar bayan zaben 2019

- Yanzu dai shirin da ake yin a kara albashi ya lafa a kasar

Mun samu labari cewa fitaccen Sanatan nan Kwamared Shehu Sani mai wakiltar yankin Kaduna ta tsakiya yayi magana a game da batun da ake tayi a kan karin albashin ma’aikata a Najeriya wanda yanzu aka ji shiru.

Tuni dai aka kammala aikin karin karancin albashi a Najeriya, inda aka mikawa shugaban kasa Muhammadu Buhari wannan kudirin domin ya sa hannu, amma har yanzu shugaban kasar bai rattaba hannun sa a kai ba.

KU KARANTA: Ministan man Najeriya yayi karin haske game da sha'anin fetur

Tun da aka ci zabe, Gwamnati tayi shiru da batun karin albashi – Shehu Sani
Sanata Shehu Sani yace an tsit da maganar karin albashi
Asali: UGC

‘Dan majalisar yake nuna cewa tun da shugaba Muhammadu Buhari ya samu lashe zaben 2019 na bana, ma’aikata ba su sake maganar karin albashi ba, bayan ya ci zabe, ganin cewa yanzu an yi tsit a kan wannan sabon kudiri.

Kawo yanzu dai ma’aikatan Najeriya da kungiyoyin kwadago su na cigaba da rokon shugaba Buhari da ya amince da karin albashin a cikin ‘yan kwanakin nan, inda shi kuma yake nuna cewa yana bin matakan ne a natse.

Sanata Sani a shafin sa na sadarwa na zamani na Tuwita yake bayyana cewa kafin ayi zaben 2019, kudirin karin albashin ma’aikata yana nan garau, amma ana kammala zaben, sai aka ga cewa farfadiya ya kama wannan kudiri

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel