Uwargidar shugaban kasa ta raba kayan tallafi ga yan gudun hijira a jahar Zamfara

Uwargidar shugaban kasa ta raba kayan tallafi ga yan gudun hijira a jahar Zamfara

Uwargidar shugaban kasa, Aisha Buhari ta kai ma jama’an da matsalar tsaro a jahar Zamfara ta shafa dauki, inda ta raba musu tallafi kayayyaki don rage musu radadin mawuyacin halin da suka tsinci kawunansu a ciki.

Legit.ng ta ruwaito Aisha ta yi wannan aikin alheri ne ta hannun gidauniyarta mai suna Future Assured, inda ta raba tallafin kayan abinci da sutura ga yan gudun hijira da adadinsu ya kai mutum dubu biyar (5,000).

KU KARANTA: Buharin dana sani a da, ba shi bane Buharin yanzu – Inji tsohon dogarin shugaba Buhari

Uwargidar shugaban kasa ta raba kayan tallafi ga yan gudun hijira a jahar Zamfara

Uwargidar shugaban kasa ta raba kayan tallafi ga yan gudun hijira a jahar Zamfara
Source: UGC

A jawabinta, wakiliyar Aisha Buhari a yayin rabon kayan, Hajiya Fadimatu Rafindadi ta bayyana cewa sun shirya wannan taimako ne domin tallafa ma mutanen da matsalar tsaro na hare haren yan bindiga ta shafa a jahar Zamfara.

Don haka ta yi kira ga jama’an dasu tashi tsaye da addu’a, tare neman Allah ya kawo karshen matsalar, sa’annan ta kara da kira ga al’ummar jahar Zamfara dasu dage da addu’ar samun zaman lafiya a jahar gaba daya.

“Na bada wannan tallafi ne domin kawo dauki ga marayu, zawara, mata da yan matan da aka kashe mazajensu da yan uwansu, don haka na shirya wannan taimako kari akan kokarin da gwamnatin jahar data tarayya suke yi na ganin an samu saukin lamarin.” Inji ta.

Shima sakataren gwamnatin jahar, Farfesa Abdullahi Shinkafi ya bayyana godiyarsa ga Aisha Buhari, tare da jinjina mata, sa’annan ya gode ma gwamnatin tarayya bisa kokarin da take na kawo ma al’ummar Zamfara dauki ta hanyoyi daban daban.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Source: Legit

Mailfire view pixel