'Yan sanda sun hallaka 'yan fashi da makami 9 a hanyar Abuja zuwa Kaduna

'Yan sanda sun hallaka 'yan fashi da makami 9 a hanyar Abuja zuwa Kaduna

Karar kwana ta cimma wasu miyagun 'yan fashi da makami 9 cikin kauyen Akilibi daura da babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna yayin wata arangama ta musayar wuta da jami'an tsaro na hukumar 'yan sanda.

Hukumar rundunar 'yan sanda ta Najeriya, ta bayar da rahoton samun nasarar hallaka miyagun 'yan fashi da makami 9 a dajin Akilbi daura da babbar hanyar Abuja zuwa Kaduna.

'Yan sanda sun hallaka 'yan fashi da makami 9 a hanyar Abuja zuwa Kaduna
'Yan sanda sun hallaka 'yan fashi da makami 9 a hanyar Abuja zuwa Kaduna
Asali: UGC

Cikin wata sanarwa a yau Lahadi da sa hannun kakakin rundunar 'yan sanda na kasa, DCP Frank Mba, ya ce hukumar ta yi galaba a kan masu ta'ada yayin wata musayar wuta da ta auku tsakanin su a ranar 10 ga watan Afrilu.

Mba ya ce hukumar ta samu nasarar cafke wasu miyagun makamai da suka hadar da nau'ikan bindigu daban-daban tare da kwanson alburusai da harsashai. Ya ce jami'in dan sanda guda ya raunata yayin artabu da masu tayar da zaune tsaye inda a halin yanzu ya ke jinya a gadon asibiti.

KARANTA KUMA: Mun aminta da matakin karatu na shugaba Buhari - INEC

Kakakin rundunar ya ce mukaddashin sufeto janar na 'yan sanda Muhammadu Adamu, ya bayyana gamsuwa dangane da kwazo da kuma nasarori da hukumar 'yan sandan ta samu musamman a yayin ci gaba da yakar ta'adar garkuwa da mutane da sauran miyagun laifuka.

Sufeton 'yan sanda ya yi kira na neman hadin gwiwar sauran hukumomin tsaro cikin gaggawa wajen yakar ta'addancin masu ta'ada da ya zamto karfen kafa a wasu sassan da dama na kasar nan.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel