Boko Haram: Rayukan Yara 432 sun salwanta a Arewa maso Gabas cikin shekarar 2018 - UNICEF

Boko Haram: Rayukan Yara 432 sun salwanta a Arewa maso Gabas cikin shekarar 2018 - UNICEF

Majalisar dinkin duniya reshen kula da harkokin yara UNICEF, ta bayyana cewa al'amura na ta'addancin Boko Haram ya kar tare da kassara Yara 432 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya cikin shekarar 2018 da ta gabata.

Majalisar dinkin duniya reshen kulawa da harkokin kananan Yara UNICEF, ta ce mummunar ta'ada ta kungiyar masu tayar da kaya baya na Boko Haram ta kassara kimanin Yara 432 a yankin Arewa maso Gabashin Najeriya cikin shekarar 2018 da ta gabata.

Boko Haram: Rayukan Yara 432 sun salwanta a Arewa maso Gabas cikin shekarar 2018 - UNICEF

Boko Haram: Rayukan Yara 432 sun salwanta a Arewa maso Gabas cikin shekarar 2018 - UNICEF
Source: Depositphotos

Babbar jami'ar sadarwa ta UNICEF, Eva Hinds, ta bayar da shaidar hakan cikin wata sanarwa a ranar Juma'a yayin tunawa da sace 'yan Mata fiye da 100 na Makarantar Sakandire ta garin Chibok dake jihar Borno shekaru biyar da suka gabata.

Ta ce ta'addancin kungiyar Boko Haram ya salwantar da rayukan kananan Yara 432, garkuwa da 180, gami da kananan yara Mata 43 da aka keta masu haddi da cin zarafi cikin shekarar bara a yankin Arewa maso Gabas.

Hinds cikin zayyana jawabai ta bayyana cewa, kungiyar mai mummunar ta'ada ta ribaci kimanin kananan Yara fiye da 3,500 wajen cin kasuwar ta'addanci na kai hare-hare daha shekarar 2013 kawowa yanzu.

KARANTA KUMA: Buhari a take-taken sa Musulmi zai bari ya ci gajiyar kujerar sa - MASSOB

Kamar yadda majaiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, Hinds ta yi kira na neman wakilin UNICEF reshen Najaeriya, Muhammad Malick Fall, da ya shimfida tsare-tsare na ingancin kare martaba da kuma 'yancin kananan yara.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Source: Legit

Online view pixel