Ya kamata matasa su hada kansu a harkar siyasa

Ya kamata matasa su hada kansu a harkar siyasa

- An bukaci matasa su fada harkar siyasa a kasar nan

- Bukatar hakan ta fito daga bakin tsohon dan takarar shugaban kasa Dr. Thomas Wilson Ikubese

Tsohon dan takarar shugaban kasa sannan kuma mai bada shawara a kungiyar nan ta YesWeFit, Dr. Thomas-Wilson Ikubese, ya bukaci matasan Najeriya da su hada kansu akan jam'iyya daya domin karbar mulki daga hannun tsofaffin 'yan siyasar kasar nan.

Ikubese ya yi wannan bayanin ne a lokacin da ya ke hira da manema labarai a tashar talabijin din channels, jiya Juma'a da safe.

Ya kamata matasa su hada kansu a harkar siyasa
Ya kamata matasa su hada kansu a harkar siyasa
Source: Twitter

Ya bukaci matasan Najeriya da su yi amfani da wannan damar domin samun mukamai manya a cikin wannan gwamnati, inda hakan zai sa a dama dasu a kasar nan, sannan kuma za su samu damar kawo cigaba a kasar nan.

Sannan ya yi Allah wadai da halayen wasu daga cikin matasan kasar nan, wadanda suke sa son zuciyarsu fiye da komai, domin samun wata bukata ta kansu.

KU KARANTA: Atiku na cikin tsaka mai wuya

Bayan haka ya yi Allah wadai da hanyar da wasu daga cikin manyan kasar nan suke bi na sanya al'umma cikin wahalar yunwa da talauci.

Da aka tambayeshi ko yana ganin matasan kasar nan za su iya kwace mulki daga hannun tsofaffin 'yan siyasa, Ikubese ya ce ya na tabbacin cewa idan matasan sun tashi tsaye, abu ne mai sauki su karbi mulki a kasar nan, mutukar sun hade kansu.

Sannan ya shawarci tsofaffin 'yan siyasa da suka jima suna yi da su hakura su barwa 'yan baya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Source: Legit

Online view pixel