Abun da muka tattauna da 'yan Najeriya a Dubai - Buhari

Abun da muka tattauna da 'yan Najeriya a Dubai - Buhari

Bayan katse ziyarar da ya kai kasar Dubai, sanadiyyar matsalar rashin tsaron da ake fama da shi a yankin arewa maso yamma, shugaban kasar ya bayyana wasu muhimman abubuwa da ya tattauna da 'yan Najeriya wadanda kasuwanci da aiki ya kai su suke zama a Dubai

Bayan dawowar shi daga ziyarar da ya kai zuwa hadaddiyar daular larabawa (UAE), shugaban kasa Muhammadu Buhari ya bayyana abubuwan da suka tattauna da 'yan Najeriya mazauna kasar Dubai din.

"Tafiya ta zuwa Dubai ya bani wata dama dana tallata Najeriya a matsayin kasar da kowacce kasa ta duniya za ta shigo dan sanya hannun jari.

Abun da muka tattauna da 'yanNajeriya a Dubai - Buhari
Abun da muka tattauna da 'yanNajeriya a Dubai - Buhari
Asali: Facebook

Sannan ya kara da cewa a taron da ya yi da 'yan Najeriya da suke zaune a Dubai, "an tambayeni akan menene manufar gwamnatin da zan kafa nan gaba. Sabuwar gwamnatin mu za ta yi kokari ganin ta kammala dukkanin ayyukan da ta fara a shekaru hudun da suka gabata, sannan kuma zata yi kokarin cika dukkanin alkawuran da ta dauka a lokacin yakin neman zabe, wanda suka hada da matsalar tsaro, da matsalar tattalin arziki.

KU KARANTA: Bankin musulunci ya bawa gwamnatin Najeriya dala miliyan 532

"Matsalar da ke faruwa a yankin arewa ta yamma, ita ce abinda muka sa gaba a wannan lokacin. Zamu yi kokarin kawo karshen kashe-kashe da kuma matsalar tsaro a yankin. Bayan haka kuma mun bada umarnin rufe duk wani wurin da ake hakar ma'adanai a yankunan da abin ya shafa. Sannan kuma zamu kawo karshen rikicin makiyaya da manoma da ake fama dashi shekara da shekaru a kasar nan.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel