Fashewar Bam ta hallaka Mutane 5, 45 sun jikkata a Maiduguri

Fashewar Bam ta hallaka Mutane 5, 45 sun jikkata a Maiduguri

Hukumar bayar da agajin gaggawa reshen jihar Borno, SEMA, ta ce rayukan Mutane biyar sun salwanta yayin da kimanin 45 su ka jikkata a sanadiyar wani mummunan hari na 'yan kunar bakin wake da ya auku a ranar Lahadi.

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa, harin 'yan kunar bakin wake na tayar da wasu bama-bamai ya salwantar da rayukan Mutane biyar nan take yayin da mutane fiye da 40 suka raunata a wajen gari na birnin Maiduguri.

Shugaban hukumar mai kula da harkokin yada rahotanni na gaggawa, Mista Kachalla Usman, ya bayar da shaidar aukuwar wannan mummunan lamari yayin wata hirar sa da 'yan jaridar na kamfanin dillancin labarai na kasa a birnin Maiduguri.

Fashewar Bam ta hallaka Mutane 5, 45 sun jikkata a Maiduguri
Fashewar Bam ta hallaka Mutane 5, 45 sun jikkata a Maiduguri
Asali: UGC

Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, harin ya auku ne a yayin da wasu Mata biyu 'yan kunar bakin wake sanye da rigunan bama-bamai suka tayar da su a cikin dandazon al'umma na yankin Muna Dalti a garin na Maiduguri.

Mista Kachalla ya ce rayukan Mutane biyar da suka hadar da 'yan kunar bakin waken biyu sun salwanta yayin da kimanin mutane 45 suka jikkata biyo bayan fashewar bama-bamai. Mutane biyu sun riga mu gidan gaskiya bayan an garzaya da su asibiti.

KARANTA KUMA: An fara siyasantar da kashe-kashen da ke aukuwa a Kaduna da Zamfara - Buhari

A cewar babban jami'in na hukumar SEMA, an garzaya da wadanda suka jikkata zuwa babban asibitin Miaduguri inda a halin yanzu su ke samun kulawa da kyakkyawar tarairaya ta kwararrun kiwon lafiya.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel