Hanyoyi guda 6 da za a bi don samawa kai sassaucin zafi a wannan lokaci

Hanyoyi guda 6 da za a bi don samawa kai sassaucin zafi a wannan lokaci

A dai dai lokacin da ake fama da tsananin zafi a Najeriya, da wasu kasashe da suke makwabtaka da ita, majiyarmu LEGIT.NG ta samo wasu hanyoyi guda 6 da idan mutum ya bi zai samu sassaucin zafin da ake fama da shi.

Mutane da yawa suna jin dadin yanayi irin na zafi, amma kuma idan zafin ya yi yawa yana iya zama damuwa, saboda zafi ya na iya zama barazana ga lafiyar mutum. Wannan yanayi da ake ciki a Najeriya ya sanya mutane da dama cikin tashin hankali, musamman wuraren da babu isasshiyar wutar lantarki, wacce zata ba su damar amfani da fanka, ko na'urar sanyaya daki domin samun sauki.

Zafi idan ya yi yawa kuma ba a dauki wani kwakkwaran mataki ba ya kan zamo matsala ga jikin dan adam.

Hanyoyi guda 6 da za a bi don rage zafi a wannan lokaci
Hanyoyi guda 6 da za a bi don rage zafi a wannan lokaci
Asali: Depositphotos

Hakan ne ma ya sanya majiyarmu LEGIT.NG gabatar da wani bincike, inda ta samo hanyoyi guda shida da za abi domin kare kai daga tsananin zafin

Hanyoyin su ne kamar haka:

1. Shan Ruwa: - Yawaita shan ruwa, ko da kuwa mutum baya jin kishin ruwa. Sannan a rage shan lemuka na kwalba ko na kwali wadanda su ke da sinadari mai karfi, a rage shan giya da suga.

2. Sutura: A dinga saka kaya wadanda ba su da nauyi, sannan a dinga amfani da kaya wadanda aka yi su da audiga, saboda suna taimakawa wurin sanyaya jikin dan adam. A dinga amfani da gilashi na ido, da hula wacce zata kare kan mutum daga rana.

3. Kwanciya: - A rage yawan zirga-zirga musamman da rana, a dinga zama a inuwa, sannan a dinga samun isashen hutu da bacci.

KU KARANTA: Yadda mijina ya gamu da ajalinshi a garin yi wa ma'aurata sulhu

4. Abinci: - A dinga cin abinci marar nauyi akai akai. Sannan a daina cin abinci mai nauyi, saboda yana karawa jikin mutum zafi.

5. Abokai: - Kada a dinga barin yara a waje ko a cikin mota. A yawaita duba mutane wadanda basu da lafiya, da tsofaffi; saboda suna iya shiga cikin wata matsala ba tare da an sani ba.

6. Wanka: - A yawaita yin wanka a duk lokacin da jiki ya dauki zafi, idan har an san za a jima a waje, a jika tawul da ruwa a dinga amfani da shi a duk inda za a je. A dinga zama a cikin gida duk lokacin da yanayin zafin ya yi yawa, musamman ma idan akwai na'ura mai sanyaya wuri.

Fanka ta kan taimaka a wasu lokutan, amma duk lokacin da yanayin ya yi tsanani da yawa bata rage komai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel