2019: Kotun sauraron karar zaben Jihar Kano ta fara zama yau

2019: Kotun sauraron karar zaben Jihar Kano ta fara zama yau

Kawo yanzu kotun da zai saurari kara game da zaben jihar Kano da aka gudanar kwanan nan, ya samu korafe-korafe har 33 a kan zabukan ‘yan majalisar dokoki da ‘yan majalisun tarayya na jihar.

Alkali Nayai Aganaba wanda shi ne shugaban wannan kotu ya bayyana wannan a zaman da aka soma yau Alhamis 4 ga Watan Afrilu a cikin Garin Kano. Nayai Aganaba ya bayyana cewa ba su samu wani korafi game da zaben gwamna ba.

Shugaban wannan kotu na musamman yayi kira ga wadanda ka kawo kukan su gaban koty da su bada hadin kai domin an karkare duk shari’ar da ke gaban kuliya nan da kwanaki 180 da dokar kasa ta kebewa wannan kotun na karar zabe.

Wannan babban Alkalin da zai gudanar da shari’a a game da zabukan da aka yi a jihar Kano yayi alkawari cewa zai yi gaskiya bakin gwargwadon iyawar sa. Sauran Alkalan da za su yi wannan shari’a su ne Ashu Augustine da Mustafa Tijjani.

KU KARANTA: Abba Gida-Gida ya samu nasara a Kotun daukaka kara

2019: Kotun sauraron karar zaben Jihar Kano ta fara zama yau
'Dan takarar PDP bai shigar da kara a kan zaben Kano ba tukuna
Asali: Twitter

Manema labarai sun bayyana cewa Kwamishinan shari’a na jihar Kano watau, Ibrahim Mukhtar, yayi alkawarin bada duk wasu goyon baya da ake bukata na jami’an tsaro da kuma wurin zama ayi aiki domin sauraron karar zaben na Kano.

Shi ma shugaban kungiyar Lauyoyi na Najeriya na reshen jihar Kano, Lawal Musa ya bayyana cewa ‘Ya ‘yan kungiyar sa za su bada hadin-kai. Shugaban kungiyar na NBA yayi kira ga Lauyoyi su guji bata lokaci domin ayi maza a tike shari’ar.

Kwanakin baya wani daga cikin Magoya bayan PDP a Kano ya bayyana cewa su na cigaba da tattara hujjoji ne domin dumfarar kotu da isassun shaida yadda za su samu damar karbe nasarar da Gwamna Abdullahi Ganduje ya samu a zaben.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel