‘Daliban Jami’ar Imo sun mutu su na aikin assha a cikin daki

‘Daliban Jami’ar Imo sun mutu su na aikin assha a cikin daki

Jama’a sun tashi da wani abin tsoro a jihar Imo inda aka wayi gari da labarin wasu ‘Dalibai 2 da ke karatu a jami’ar kimiyya da fasaha ta tarayya da ke Garin Owerri sun mutu wajen tarawa da Budurwa.

Jami’an ‘Yan Sanda sun tabbatar da aukuwar wannan abu a Ranar Laraba 3 ga Watan Afrilun 2019. Kakakin Rundunar ‘yan sanda na jihar Imo, Orlando Ikeokwu, yace su na zargin wadannan Samari da amfani da miyagun kwayoyi.

Binciken ‘Yan sanda ya nuna cewa wadannan Samari sun mutu ne bayan da su ka shaki kwayoyin hauka lokacin da su ke tarawa da wata Yarinya a cikin daki. Sunan wadannan Dalibai Ugochukwu Kingsley da kuma wani Richard.

KU KARANTA: Kwastam sun tara Biliyan 3 da wasu kaya rututu a cikin wata 3

Jami’an tsaron sun bada sunan Na-uku cikin wadannan Samari da suna Aka Uche yayin da ita kuma Yarinyar da ake nema sunan ta Onyinyechi Okafor. Yanzu dai ita Okafor da kuma Uche mai shekaru 27 su na faman jinya a asibiti.

Sai dai ta tabbata cewa Kingsley da kuma Richard sun mutu yayin da su ke wannan aiki. Wannan abu ya faru ne a wani gida da ake kira Sunshine Lodge, da ke cikin Unguwar Ihiagwa wanda ke kusa da jami’ar tarayyar ta Garin Owerri.

Orlando Ikeokwu yace duka wadannan Bayin Allah, dalibai ne na jami’ar ta FUTO da ke jihar Imo. Ikeokwu yace an samu Matasan tsirara ne tare da wasu kayan maye da ake zargi da tabar wiwi. Tuni dai aka ajiye gawar su asibiti.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Source: Legit

Mailfire view pixel