Rikicin kabilanci: An kashe mutum biyu, an kona gidaje 38 a Nasarawa

Rikicin kabilanci: An kashe mutum biyu, an kona gidaje 38 a Nasarawa

An kashe mutane biyu tare da kone gidaje 38 a wani rikicin kabilanci da ya barke a garin Andaha da ke karkashin hukumar Akwanga ta jihar Nasarawa.

Mazauna kauyuka uku da ke kusa da garin da rikicin ya faru sun kaurace wa gidajen su saboda tsoron kai harin daukan fansa a kan su. Mutanen sun fara kauracewa gidajen su ne bayan samun rahoton kashe wata budurwa mai shekaru 19 da ake zargin wasu makiyaya da aikata wa.

Kakakin rundunar 'yan sanda a jihar Nasarawa, Samaila Usman, ya tabbatar da afkuwar rikicin ga gidan Talabijin na Channels a hirar su da shi ta wayar tarho.

A cewar sa, rikicin ya samo asali ne bayan wasu da ake zargin makiyaya ne sun yiwa wasu mata uku 'yan kabilar Mada fyade yayin da suke dawowa daga wurin wani biki da suka halarta a garin Katanza.

Rikicin kabilanci: An kashe mutum biyu, an kona gidaje 38 a Nasarawa
Gwamnan jihar Nasarawa; Umar Tanko Al-Makura
Asali: UGC

Kakakin ya bayyana cewar makiyayan sun lakada wa Joy Danlami; daya daga 'yan matan da suka yiwa fyade, duka, lamarin da ya yi sanadiyar mutuwar ta.

"Wasu makiyaya sun kai wa wasu 'yan matan kabilar Mada hari a hanyar su ta dawowa daga wurin biki, sun yiwa wata mai suna Joy Danlami fyade sannan nan sun lakada ma ta duka.

DUBA WANNAN: 'Yan bindiga sun sace dan asalin kasar Koriya ta Arewa a Zamfara

"Y'an uwanta sun dauke ta zuwa babban asibitin garin Akwanga inda daga bisani ta mutu. Hakan ne yasa matasan kabilar Mada suka hada kan su tare da kai hari sansanin makiyaya inda suka kashe mutum daya sannan suka kone wurin.

"Daga baya su ma makiyayan sun hada kai tare da kai harin daukan fansa a kauyukan Nidam da Maite, inda suka kone gidaje masu yawa," a cewar Usman.

Kafin afkuwar wannan rikici, jama'ar garuruwan Nidam, Maite da Katanza na zaune cikin lumana da juna na tsawon shekaru masu yawa.

Wasu mazauna yankin da suka tattauna da majiyar mu, sun yi kira ga gwamnati da ta kawo masu dauki domin kare afkuwar wani rikicin a nan gaba.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel