APC ta tsayar da Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa

APC ta tsayar da Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa

- A kokarin da wasu Sanatocin jam'iyyar APC suke na ganin sun samu damar hayewa kujerar majalisar dattijai, sai gashi jam'iyyar APC ta fito da Ahmad Lawan a matsayin zabinta

- Hakan ya baiwa da yawa daga cikin Sanatocin mamaki, inda babu shiri suka fara neman manyan mukamai a cikin majalisar

APC ta tsayar da Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa
APC ta tsayar da Ahmad Lawan a matsayin shugaban majalisar dattawa
Asali: Depositphotos

A jiya ne jam'iyyar APC ta tsayar da Ahmad Lawan, a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa. Hakan ya biyo bayan wani taro da jam'iyyar ta APC ta hada a fadar shugaban kasa, inda shugaban kasa Muhammadu Buhari, shugaban jam'iyyar APC ta kasa, Comrade Adams Oshiomhole, da wasu gwamnonin APC guda 11, suka samu damar halartar taron.

Majiya mai karfi ta tabbatar da cewa, shugaban jam'iyyar APC, Adams Oshiomhole, shine ya bayyana bukatar su ta tsayar da Ahmad Lawan din, a gaban sauran Sanatoci guda uku, wadanda suke da burin hawa kujerar.

Sanatocin sun hada da; Sanata Ali Ndume (Borno), Sanata Danjuma Goje (Gombe) da kuma Sanata Abdullahi Adamu (Nasarawa).

A daren jiyan Sanata Bello Mandiya ya tabbatarwa da manema labarai cewa jam'iyyar APC ta tsayar da Sanata Ahmad Lawan din a matsayin dan takarar ta.

KU KARANTA: Yanzu-yanzu: An soke zaben gwamnan jihar Zamfara tare dana sauran 'yan majalisun jihar da suke jam'iyyar APC

Wani Sanata da bai so a bayyana sunanshi ba shima ya ta tabbatar da hakan. Inda ya ke cewa:

"Munyi mamaki da muka ji shugaban jam'iyya ya bayyana Ahmad Lawan a matsayin Shugaban Majalisar Dattawa. Sannan kuma babu wanda aka bari yayi magana a cikin mu sai aka ce an tashi daga taron. "

Idan ba a manta ba a shekarar 2015, Sanata Ahmad Lawan ne jam'iyyar APC ta so ta tsayar a matsayin shugaban majalisar dattawa, sai aka samu akasin haka, inda tsohon shugaban majalisar dattawan Sanata Bukola Saraki ya fito tare da goyon bayan 'yan jam'iyyar PDP na wancan lokacin suka karbe kujerar.

Gwamnonin da suka samu damar halartar taron sun hada Kebbi, Zamfara, Plateau, Jigawa, Kaduna, Lagos, Osun, Oyo, Borno, Yobe da kuma jihar Kogi. Sai kuma Sakataren Tarayya, Boss Gida Mustapha, shima ya samu damar halartar taron.

Sannan sai Sanatan jihar Anambra, wanda ya lashe zabe a jam'iyyar (YPP), Sanata Ifeanyi Ubah, shima ya halarci taron.

Oshiomhole yace daga cikin Sanatoci 16 da suka bar jam'iyyar APC, Sanata Dino Melaye ne kawai ya samu damar komawa kujerar shi. Ya kara da cewa gaskiya yanzu baza su ji dadin zaman majalisa ba, tunda babu 'yan barkwanci a cikin su.

A karshe ya bayyana Sanata Ifeanyi Ubah, a matsayin mai hangen nesa, a kokarin da yake na dawowa jam'iyyar ta APC.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel