Safarar miyagun kwayoyi: An kama wani da buhunnan Tramadol uku a Kano

Safarar miyagun kwayoyi: An kama wani da buhunnan Tramadol uku a Kano

An kama wani dan Najeriya mai suna Sahabi Adamu dauke da buhunna uku na haramtattun kwayoyin Tramadol da kudinsu ya kai Naira Miliyan 30 a garin Kano.

Jami'an Hukumar Kwastam na Najeriya, NCS, na Zone B ne suka kama shi a hanyar Kano zuwa Hadejia kamar yadda Daily Trust ta ruwaito.

Shugaban Kwastam na shiyyar Zone 'B' Kaduna, Sarkin Kebbi Mustafa ya ce an samu katon 1,1146 na Tramadol masu nauyin 225mg a cikin buhunna uku da aka kama Adamu da shi.

Safarar miyagun kwayoyi: An kama wani da buhunnan Tramadol uku a Kano
Safarar miyagun kwayoyi: An kama wani da buhunnan Tramadol uku a Kano
Asali: UGC

Ya ce wanda aka kama ya bayyana cewa ba shi kadai ne ya ke wannan mummunan sana'ar ba kuma ya yi alkawarin bawa jami'an tsaro hadin kai ta hanyar basu bayanai da za su kai ga kama sauran abokan huldarsa.

DUBA WANNAN: CP Mohammed Wakili 'Singham' ya nemi afuwar kungiyar NBA reshen Kano

A wani labarin, Legit.ng ta kawo muku cewa Yan bindiga sun kashe wani ma'aikacin lafiya mai sun Mr Audi Gada mai shekaru 43 a karamar hukumar Shongom na jihar Gombe a ranar Laraba 20 ga watan Maris.

Gada ma'aikaci ne da cibiyar kula da lafiya bai daya da ke kauyen Bagunji.

'Yan bindigan da aka ce adadin su ya kai 13 sun kai farmaki a kauyen ne da safiyar ranar Laraba kuma suka harbe Gada kuma suka yiwa matarsa Lami rauni.

Dan uwan marigayin, Umar B Alhaji ya shaidawa Daily Trust a wayar tarho cewa 'yan bindigan sun kai farmaki kauyen ne misalin karfe 12.30 na dare inda suka harbe Gada suka kuma yi tafiyarsu ba tare da sun dauki komi a gidansa ba.

Kakakin rundunar 'yan sanda na jihar, Mary Malum ta ce ba ta da masaniya a kan afkuwar lamarin a lokacin da aka tuntube ta domin ji ta bakin ta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel