Alkali ya bada umarni a sauke Sarkin Efut na Kalaba daga kan mulki

Alkali ya bada umarni a sauke Sarkin Efut na Kalaba daga kan mulki

Babban Kotun jihar Kuros Riba ta bada umarnin tsige Mai martba Sarkin kasar Efuts da ke cikin karamar hukumar Kalaba ta kudu a jihar. Jaridar Daily Trust ta rahoto wannan a Ranar 20 ga Watan Maris.

Kotun ta yanke wannan hukunci ne bayan wani zama ada tayi a Ranar Larabar nan da ta gabata, Alkali mai shari’a Edem Ita Kooffreh ya nemi Mai martaba Fardesa Hogan Itam yayi maza ya bar karagar mulkin da yake kai a yanzu.

Bugu da kari kuma kotun tace ka da ta sake jin labarin Mai martaban ya sake aikata wani abu da sunan Sarkin kasar Efuts. A shari’ar mai lamba ta HC/442/2018, Alkalin kotu ya bayyana cewa bai halatta Sarkin ya cigaba da mulki ba.

Kotu ta jawo sashen da ke magana a kan harkar sarautar gargajiya a cikin kundin tsarin mulkin Najeriya da kuma dokokin jihar ta Kuros Riba na 2004. Kotu tace an samu tangarda wajen yadda aka nada Hogan Itam a kan kujerar sarauta.

KU KARANTA: 2019: Matakin da Kotu ta dauka yayi wa Jam’iyyar PDP ciwo a Jihar Bauchi

Alkali ya bada umarni a sauke Sarkin Efut na Kalaba daga kan mulki
Kotu ta bada umarnin tsige Sarkin Efut daga mulki
Asali: Depositphotos

Bisa ga hukuncin kotun, Mai martaban zai bar kan kujerar sarautar da yake kai da gaggawa sannan kuma ya sauka daga matsayin sa na shugaban Sarakunan kasar Kalaba. Shi dai Sarkin ya tubure yace har yanzu bai san da maganar ba.

A bara ne gwamna Ben Ayade na jihar ya mikawa Mai martaban takardar da ke tabbatar da sarautar sa bayan an yi shekaru fiye da 10 ana ta faman ta-ta-bur-za a kan gadon mulki. Tuni wasu masu neman kujerar su ka nuna rashin yardar su.

Etubom Nyong Effiom Okon da kuma wasu mutane 5 ne su ka maka Sarkin a kotu inda su ka kai kukan cewa nadin da aka yi masa ya sabawa shari’a don haka a tsige sa. Yanzu dai kotu ta yanke hukunci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel