Abin da likitoci su ka fada bayan ‘yar Najeriya ta haifi ‘ya’ya 6 a asibitin Amurka

Abin da likitoci su ka fada bayan ‘yar Najeriya ta haifi ‘ya’ya 6 a asibitin Amurka

Wata mata mai suna Chiaka Thelma, ‘yar asalin Najeriya, ta haifi ‘ya’ya 6 rigis a wani asibitin kasar Amurka da ke jihar Texas yayin hutun karshen mako.

A cewar asibitin, ta shafinsa na Tuwita, da kyar ake samun faruwar irin wannan haihuwa. Ana samun irin haihuwar sau daya a cikin haihuwa biliyan 4.7.

Asibitin ya kara da cewa akwai maza hudu da mata biyu daga cikin jariran 6 da Thelma ta haifa, kuma ta haife su ne tsakanin karfe 4:50 zuwa 4:59 na safiya.

Sanarwar asibitin ta kara da cewa dukkan jariran na cikin koshin lafiya kuma sun a cigaba da samun kulawa a sashen karbar haihuwa na asibitin.

Tuni mahifiyar jariran ta saka wa matan biyu suna, Zina da Zuriel yayin da ta ce tana cigaba da neman sunayen da ya dace ta saka wa ragowar jariran maza hudu.

Abin da likitoci su ka fada bayan ‘yar Najeriya ta haifi ‘ya’ya 6 a asibitin Amurka
Thelma; ‘yar Najeriya da ta haifi ‘ya’ya 6 a asibitin kasar Amurka
Asali: Twitter

Wannan abun al’ajabi na haihuwar ‘ya’ya 6 da Thelma ta yin a zuwa ne a daidai lokacin da wata jami’ar kasar Ingila dake garin Kent ta bayyana cewar ta gudanar da wani bincike dake nuna cewar nan bada dadewa ba maza zasu kare, su gushe daga doron kasa tamkar ba a taba halittar su ba.

Kwararren masanin kimiyya jami’ar Kent, Darren Griffin, ya bayyana cewar maza zasu kare ne saboda kwayar halittar Y, dake rikidewa zuwa namiji yayin haduwar maniyyin mace da namiji lokacin daukar ciki, zai kare, wanda hakan daidai yake da gushewar maza daga doron kasa.

DUBA WANNAN: Zaben 2019 a Najeriya mummunan labari ne ga dimokradiyya – Amurka

Batun lamarin karewar kwayar halittar Y dake cikin maniyyi na cigaba da tayar da hankulan masu bincike a bangaren kimiyya musamman ganin cewar kwayar halittar day ace tal a jikin mutum kuma babu madadin ta.

Masana sun bayyana cewar daga cikin abubuwan da zasu jawo karewar kwayar halittar Y a jikin bil’adama akwai kwankwadar barasa (giya) dake hana kwayar ta cigaba da haihuwa na tsawon shekaru kamar yadda ragowar kwayoyin halitta ke haihuwa da sabunta kan su.

Wannan dalilin ne yasa Griffin bayyana cewar akwai yiwuwar karewar kwayar halittar Y gaba daya a doron kasa.

Sakamakon binciken na Griffin ya saka masana da ma su nazari yin tambayar ko yaya rayuwa zata kasance idan babu maza a duniya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel