Shugaban kasar Koriya ta Kudu ya taya shugaba Buhari murnar samun nasarar tazarce
Shugaban kasar Koriya ta Kudu, Moon Jae-in, ya taya shugaban kasa Muhammadu Buhari murnar samun nasarar tazarce yayin zaben kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairun 2019.
Mai magana da yawun shugaban kasa Buhari, Mallam Garba Shehu, shi ne ya bayyana hakan a yau Talata yayin ganawa da manema labarai a fadar shugaban kasa ta Villa da ke garin Abuja.
Mallam Shehu ya ce, shugaban kasa Jae-in cikin wata rubutacciyar wasika da ya aike da ita a madadin sa da kuma al'ummar kasar Koriya ta Kudu, ya taya shugaban kasa Buhari murnar samun nasarar tazarce.
Cikin wasikar sa shugaba Jae-in ya yi fatan Najeriya za ta samu kyakkyawar makoma ta ci gaba musamman a fannin habakar tattalin arziki a karkashin jagorancin shugaban kasa Buhari.
KARANRA KUMA: Atiku ya shigar da manyan korafi 5 domin kalubalantar sakamakon zabe
Ya bayyana farin cikin sa dangane da yadda Najeriya da kasar Koriya ta Kudu ke ci gaba da cin moriyar kyakkyawar alaka a tsakanin su gami da hadin kai tun a shekarar 1980.
Shugaba Jae-in ya yi fatan son barka da kuma arziki na lafiya ga shugaban kasa Buhari a yayin da daura damarar tabbatar da kyakkyawar makoma a jamhuriyyar Najeriya.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na dandalan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng