Babban dalilin da yasa nake kira a zabi Ganduje – Inji Sheikh Kabiru Gombe

Babban dalilin da yasa nake kira a zabi Ganduje – Inji Sheikh Kabiru Gombe

Babban Malamin addinin Musulunci, kuma sakataren kungiyar Jama’atil Izalatil Bidi’a wa Iqamatissunnah, Sheikh Kabiru Gombe ya bayyana wata kwakkwaran dalilin da ya kamata jama’an jahar Kano su sake zaban Gwamna Abdullahi Ganduje a karo na biyu.

Legit.ng ta ruwaito Kabiru ya bayyana haka ne cikin wani jawabi da yayi kuma aka nada, da a yanzu haka yake yawo a kafafen sadarwar zamani ana watsa shi, inda yace babban dalilin da zai fada ma Allah idan Ya tambayeshi akan me yace a zabi Ganduje shine Musuluntar da Maguzawa.

KU KARANTA: Wata sabuwa: Faruk Lawan ne ya keta sakamakon zaben gwamnan Kano – Inji Kwamishina

Babban dalilin da yasa nake kira a zabi Ganduje – Inji Sheikh Kabiru Gombe
Ganduje da Sheikh Kabiru Gombe
Asali: UGC

A jawabin nasa, Shehin Malamin ya bayyana yadda Gwamna Ganduje ya taba gayyatarsu zuwa Musuluntar da wasu maguzawa su dari biyu, da kiristoci guda biyu da suka nuna sha’awar shiga Musulunci.

“Allah Ya sani kuka na dinga yi a ranar da muka tafi musuluntar da maguzawan, saboda naga abinda ban taba gani ba, na san irin wahalar da muke sha idan muka shiga garin arna ko maguzawa kafin mu samu mutum 10 sun karbi musulunci, tare da bata tsawon lokaci. Amma sai gashi abin mamaki mutane 202 zasu musulunta a gabana, zasu karbi Kalmar shahada.” Inji shi.

Malam Kabiru ya kara da cewa shi da kasan mutane 20 ta baiwa shahada, shima shugaban kungiyar Izala, Sheikh Abdullahi Bala Lau mutane 30 ya baiwa shahada, sai gwamnan jahar Kano daya baiwa kusan mutane 50 shahada, haka nan Shekarau ma ya bada shahada ga mutane 30.

Malamin yace haka sauran Maluma suka biyo baya suka yi ta baiwa maguzawanann Kalmar shahada, anayi ana canza musu suna, inda suke zaban sunan daya kwanta musu na Musulunci, har yace a gabansa wani mutumi ya bayyana musu cewa sunansa na yanka Jemage.

Daga karshe shehin Malamin ya tabbatar da cewa bayan kammala musuluntar da maguzawan, sai Ganduje ya raba musu kyautan kayan alheri, inda mata suka samu turmin zani da atamfa da jarin kudi, Maza kuma suka samu turmin shadda da jari.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng