Sarakuna daga jihohin arewa uku sun ziyarci Buhari, sun nemi ya kirkiri jihar Borgu (Hoto)

Sarakuna daga jihohin arewa uku sun ziyarci Buhari, sun nemi ya kirkiri jihar Borgu (Hoto)

Jama’ar Borgu da ke jihohin Neja, Kebbi da Kwara sun ziyarci shugaban kasa Muhammadu Buhari a jiya, Alhamis, tare da mika butar su ta neman jihar Borgu gare shi.

Sarkin Borgu, Alhaji Muhammed Haliru Dantoro, ne ya jagoranci tawagar wakilan jama’ar Borgu zuwa fadar shugaban kasa, Villa, da ke Abuja, domin taya shi murnar samun nasarar lashe zabe a karo na biyu.

Manyan sarakunan gargajiya na Borgu da ‘yan siyasa irin su mai Magana da yawun majalisar dattijai, Sanata Sabi Abdullahi na jam’iyyar APC daga jihar Neja, na daga cikin tawagar.

Sarakuna daga jihohin arewa uku sun ziyarci Buhari, sun nemi ya kirkiri jihar Borgu (Hoto)
Wakilan jama'ar Borgu
Asali: Twitter

Sarkin ya shaidawa Buhari cewar jama’ar Borgu a jihohin Neja, Kebbi, da Kwara kan su a hade yake wajen neman a basu jihar su ta kashin kan su.

DUBA WANNAN: Rundunar ‘yan sanda ta tabbatar da mutuwar mutane 17 a Birnin Gwari

Idan har shugaban kasa na tunanin kirkirar Karin wata sabuwar jiha a Najeriya, kamata ya yi ta kasance Borgu saboda albarkatun da yankin ke da su wadanda zasu taimaki tattalin arzikin Najeriya,” a cewar sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel