Sakamakon zabe: hadimin Ganduje ya yi murabus saboda Abba Gida-Gida

Sakamakon zabe: hadimin Ganduje ya yi murabus saboda Abba Gida-Gida

Alhaji Hashim Suleiman, babban mai bawa gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje, shawara a kan raya birane, ya mika takaradar sa ta yin murabus daga mukamin sag a sakataren gwamnatin jihar Kano a yau, Laraba.

A takardar sa ta yin murabus din, ya bayyana cewar dalilinsa na dauka wannan mataki shine saboda gwamna Ganduje ya ki amincewa da kayen da dan takarar gwamnan jihar Kano a jam’iyyar PDP, Abba Kabir Yusuf, ya yi ma sa.

Suleiman ya ce Abba ne ya lashe zaben na ranar Asabar da hukumar zabe ta kasa (INEC) ta bayyana a atsayin wanda bai kammalu ba.

Sakamakon zabe: hadimin Ganduje ya yi murabus saboda Abba Gida-Gida
Ganduje da Abba Gida-Gida
Asali: UGC

A takardar da Suleiman ya rubuta da hannun sa, y ace: “na rubuta wannnan takarda ne domin sanar da kai cewar na ajiye mukamina na bayar da shawara a kan raya birane bisa radin kai na.

DUBA WANNAN: Cakwakiya: Sanarwar Orji Kalu ya ci zaben sanata a APC kuskure ne – INEC

“Ina mai godiya gare ka bisa damar ka bani na yin aiki a gwamnatin ka.”

Sannan ya kara da cewa kamata ya yi gwamnan da ke amsa sunan ‘Khadimul-Islam’ ya kasance mai rungumar kaddara da yarda da ikon Allah a duk halin da ya tsinci kan sa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel