El-Rufai ya jagoranci Gwamnonin APC zuwa gaban Shugaba Buhari a Aso Villa

El-Rufai ya jagoranci Gwamnonin APC zuwa gaban Shugaba Buhari a Aso Villa

Gwamnoni 5 na jam’iyyar APC mai mulki ne su ka gana da shugaban kasa Muhammadu Buhari jiya a fadar shugaban kasa. An yi wannan zama ne dai a bayan labule tare da wadannan gwamnonin.

Gwamna Nasir El-Rufai da wasu Takwarorin sa ne su ka yi wannan zama da shugaban kasar. Sahara Reporters tace gwamnonin da ke jam’iyyar shugaba Buhari, sun tattauna ne game da zaben Jihohin da aka dakatar a yanzu.

Gwamnonin da su ka yi wa Nasir El-Rufai na jihar Kadunarakiya su ne: Dr. Kayode Fayemi (Ekiti), Abdulaziz Yari (Zamfara), Abubakar Atiku Bagudu (Kebbi), Yahya Bello (Kogi) da kuma Gwamna Badaru Abubakar (Jigawa)

Majiyar ta Sahara Reporters tace a zaman, gwamnonin za su yi kokarin jawo hankalin shugaba Muhammadu Buhari da ya kawowa jihohin jam’iyyar APC da aka dakatar da zaben su doki domin ganin sun samu nasara.

KU KARANTA: Babu maganar tsige Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Kano kafin zabe

El-Rufai ya jagoranci Gwamnonin APC zuwa gaban Shugaba Buhari a Aso Villa
Gwamnonin APC na so Buhari ya shiga cikin lamarin Jihohin Arewa
Asali: UGC

Wani a fadar shugaban kasar ya bayyana cewa Gwamna Nasir El-Rufai da ‘Yan Tawagar na sa, za su yi yunkurin nunawa shugaba Buhari cewa Jam’iyyar APC za ta ji kunya idan har wasu Gwamnonin ta su ka sha kasa a hannun PDP.

Daga cikin inda jam’iyyar APC ke fuskantar barazana a zaben gwamno in da aka yi kwanan nan akwai Jihar Adamawa, Kano da kuma Bauchi inda duk ‘yan takarar jam’iyyar PDP ne ke kan gaba kafin hukumar INEC ta dage zaben.

Haka ma a Filato an dage zaben gwamnan har sai zuwa Ranar 23 ga watan nan. An dauki wannan mataki ne bayan la’akari da yawan kuri’un da aka soke a zaben jihohin da kuma irin tazarar da ke tsakanin jam’iyyun da ke takara.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel