Majalisar Jiha: APC ta lashe Kujeru 12, PDP ta samu 3 a jihar Kano

Majalisar Jiha: APC ta lashe Kujeru 12, PDP ta samu 3 a jihar Kano

Da sanadin shafin jaridar Daily Trust mun samu rahoton cewa, a yayin da hukumar zabe ta kasa ke ci gaba da bayyana sakamakon zaben kujerar gwamnoni da ta 'yan majalisar jiha da aka gudanar a jiya Asabar, jam'iyyar APC ta yi shigar wuri a jihar Kano.

Majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, jam'iyya mai ci ta APC ta lashe kujeru 12 cikin 40 na 'yan majalisar dokokin jihar Kano yayin da babbar jam'iyyar adawa ta PDP ta samu nasarar kujeru uku kacal.

Majalisar Jiha: APC ta lashe Kujeru 12, PDP ta samu 3 a jihar Kano
Majalisar Jiha: APC ta lashe Kujeru 12, PDP ta samu 3 a jihar Kano
Asali: Depositphotos

Cikin zayyanar sakamakon Turawan Zaben a yau Lahadi cikin hedikwatar Hukumar INEC daura da hanyar sansanin Alhazai da ke birnin Kano, jam'iyyar APC ta yi nasara a zaben 'yan majalisun dokoki masu wakilcin kananan hukumomi 12 na Kanon Dabo.

Kananan hukumomin kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya wassafa sun hadar da; Albasu, Bunkure, Madobi, Rano, Gwarzo, Dambatta, Karaye, Makoda, Sumaila, Garko, Kura, Kunchi da kuma karamar hukumar Tsanyawa.

KARANTA KUMA: Yadda sakamakon zaben gwamnan jihar Kano ke kasancewa

Jam'iyyar PDP ta yi nasara a kananan hukumomin Bebeji, Kibiya da kuma Gezawa. Kazalika jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, yayin da hukumar INEC ke bayyana sakamakon zaben gwamnan jihar Kano, ana ci gaba da fafatawa tsakanin manyan 'yan takarar biyu na jam'iyyar APC, Gwamna Abdullahi Ganduje da kuma na jam'iyyar adawa ta PDP, Abba Kabir Yusuf.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel