Ana cigaba da kirga kuri'un zaben Gwamna da 'Yan Majalisa a Kano
Mun samu labari cewa ana kirga kuri'u na zaben gwamna a jihar Kano da sauran jihohin Najeriya. Gwamna mai-ci zai samu kalubale daga jam’iyyun adawa irin su PDP da kuma jam’iyyar PRP.
Ga dai wasu daga cikin rahotannin da mu ke samu daga wasu kananan hukumomin na jihar ta Kano kawo yanzu.
1. Ungogo LG
PDP= 42, 032
APC= 26, 118
2. Rano LG
APC 16, 694
PDP 14, 892
3. Madobi LG
APC= 24, 491
PDP= 24, 309
KU KARANTA: PDP ta nemi a cafke Mukarraban Ganduje bayan sun yi ikirarin lashe zabe
4. Kibiya LG
PDP= 17, 373
APC= 15, 760
5. Bebeji LG
PDP= 18, 533
APC=17, 418
6. Gezawa LG
PDP 24, 151
APC 20, 506
KU KARANTA: An yi awon gaba da kayan aikin zaben Gwamna a Kudu
7. Albasu LGA
APC 25,358
PDP 18,441
8. Bebeji LG
APC. 17,418
PDP. 18,533
9. BUNKURE LG
APC 20,407
PDP 20,222
10. Rimin Gado
APC 19,453
PDP 13,777
KU KARANTA: Yadda sakamakon zaben sabon Gwamna a Jihar Kaduna yake kasancewa
Tuni dai gwamna Abdullahi Ganduje da Mai dakin sa watau Hajiya Dr. Hafsat Umar Ganduje su ka kada kuri’ar su a zaben na yau. Haka shi ma ‘Dan takarar jam’iyyar PRP, Salihu Takai ya kada ta sa kuri’ar a mazabar sa.
Kamar yadda mu ka ji an samu takaddama a yankin Mandawari inda magoya bayan ‘dan takarar PDP watau Abba Kabir Yusuf su ka hadu da Mabiyan APC da ke tare da shugaban jam’iyya na jihar watau Abbas Sanusi.
Kwamishin ‘yan sanda na jihar Kano watau Muhammad Wakili ya kawo ziyarar ba-zata zuwa Yankin na Mandawari da ke cikin birnin Kano domin ganin an yi zabe lafiya. Akwai dai manyan ‘yan siyasan Kano a yankin.
Haka kuma mun ji cewa dazu nan Jami’an tsaro su kayi nasarar damke wata mota cike makil da kayan zabe a wata makaranta da ke Magwan da ke cikin Yankin Gawuna inda Mataimakin Gwamnan jihar Kano mai-ci ya fito.
Ana kukan cewa ana amfani da kudi wajen sayen kuri’un jama’a yayin da a wasu wurare kuma ake kukan cewa ba a kai isassun kayan zaben da ake bukata ba kamar yadda mu ke samun labari.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT
Asali: Legit.ng