APC ta ci zaben gwamna a Jigawa da Kebbi, ba a kammala na Sokoto ba

APC ta ci zaben gwamna a Jigawa da Kebbi, ba a kammala na Sokoto ba

Sakamako na karshe da hukumar zabe mai zaman kan ta (INEC) ta bayyana a Kebbi, ya nuna cewar gwamnan jihar, Abubakar Atiku Bagudu na jam’iyyar Kebbi ya sake lashe zaben gwamnan jihar a karo na biyu.

Bagudu na jam’iyyar APC ya samu kuri’u 673,717, adadin da ya bashi nasara a kan babban hamayyar sa na jam’iyyar PDP, Sanata Isah Galaudu, wanda ya samu kuri’u 106,633, sai kuma Malam Ka’oje na jam’iyyar SDP da ya samu kuri’u 7,444.

Sakamakon zaben kujerar gwamna da hukumar zabe ta sanar a Jihar Jigawa ya tabbatar da cewar gwamnan jihar mai ci, Mohammed Abubakar Badaru, ya sake lashe zaben kujerar gwamna a karkashin inuwar jam’iyyar APC.

Badaru ya samu kuri’u 810,933 da su ka bashi nasara a kan babban abokin hamayyar sa, dan takarar jam’iyyar PDP, Malam Aminu Ibrahim Ringim, wanda ya samu adadin kuri’u 288,356, sannan sai dan takarar jam’iyyar SDP, Bashir Adamu, wanda ya zo na uku da adadin kuri’u 32,894.

APC ta ci zaben gwamna a Jigawa da Kebbi, ba a kammala na Sokoto ba
Tambuwal
Asali: UGC

Malam Aminu Ringim ne dan takarar gwamnan jam’iyyar PDP da gwamna Badaru ya fara kayar wa a zaben shekarar 2015 lokacin da jihar Jigawa ke hannun jam’iyyar PDP.

Hukumar zabe ta kasa mai zaman kan ta (INEC) ta bayyana zaben kujerar gwamna da aka yi ranar Asabar da ta gabata a jihar Sokoto a matsayin wanda bai kammalu ba.

Baturiyar zabe a jihar, Farfesa Fatima B. Mukhtar, ce ta bayyana da duku-dukun safiyar yau, Litinin, bisa hujjar cewar adadin kuri’un da aka soke ya fi adadin banbancin kuri’un da ke tsakanin ‘yan takarar biyu.

DUBA WANNAN: Ku sanar da sakamakon zaben jihar Kano - PDP ta gargadi INEC

Kamar yadda sakamakon zaben na karshe ya nuna, jam’iyyar PDP ta samu nasara da adadin kuri’u 489,558 yayin da jam’iyyar APC ke biye ma ta da adadin kuri’u 486,145.

Ana fafata wa a matakin kujerar gwamna a jihar Sokoto tsakanin gwamna mai ci, Aminu Waziri Tambuwal na jam’iyyar PDP, da babban abokin hamayyar sa, Ahmad Aliyu na jam’iyyar APC.

75,403 ne adadin kuri’un da aka soke daga mazabu 136 da ke fadin kananan hukumomin jihar Sokoto 22, kamar yadda baturiyar zaben ta sanar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel