2019: Masu harin Gwamnan Taraba sun ja baya sun bar wa PDP

2019: Masu harin Gwamnan Taraba sun ja baya sun bar wa PDP

Yayin da ake shirin zaben gwamnoni a jihohi da-dama a Najeriya, mun ji labari cewa ‘yan takara fiye da 10 da ke harin kujerar Gwamna a jihar Taraba sun janye takarar su, sun bi jam’iyyar PDP mai mulki.

‘Yan takara 15 da su ka fito neman gwamna a jihar ta Taraba sun maida wukar su inda su ka je za su goyawa gwamna mai-ci watau Darius Ishaku baya a zaben da za ayi. Wadannan ‘yan takara sun bada dalilin su na ja-baya a zaben.

Hakan na zuwa ne dai jim kadan bayan jam’iyyar APGA mai adawa ta bayyana cewa mabiyan ta za su zabi gwamna Darius Ishaku ne a zaben da za ayi a karshen makon nan. Ana tunani cewa wannan zai karawa PDP karfi a jihar.

KU KARANTA: Jam’iyyun adawa sun cin ma matsaya game da wanda za a zaba a Gombe

2019: Masu harin Gwamnan Taraba sun ja baya sun bar wa PDP
Wadanda ke neman Gwamna a Taraba sun yi wa Darius mubaya’a
Asali: Depositphotos

Daga cikin jam’iyyun da su ka fito su ka nuna cikakken bayan su ga ‘dan takaran na PDP mai rike da mulki akwai jam’iyyar hamayya ta SDP, da MAJA, LP, ZLP, NAC,MPN, PPM, NCPN, DPP, da kuma wata jam’iyya mai taken FJP.

Sauran wadanda su ka fito su ka tabbatar da mubaya’ar su kuma sun hada jam;iyyu irin su PPA, AA, da kuma jam’iyyar YDP. Wadannan jam’iyyu sun ce sun yi haka ne domin bunkasar damukaradiyya a wannan jihar ta Taraba.

Gwamna Darius Ishaku yayi farin ciki da wannan goyon baya da ‘yan adawa su ka ba sa. Kwanan nan ne dai kotu ta tsige ‘dan takarar gwamna na jam’iyyar APC mai adawa a jihar, idan ba ku manta ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel