An bude asusun neman taimako dan taimaka ma Atiku ya kai karar Buhari gaban kotu

An bude asusun neman taimako dan taimaka ma Atiku ya kai karar Buhari gaban kotu

Wani babban mai goyon bayan dan takarar shugaban kasa daga jam’iyyar PDP, Alhaji Atiku, mai suna Segun Awosanya ya bude wani asusun neman tallafin kudi don tara ma Atikun kudaden fafatawa a karar da zai shigar da Buhari saboda zaben 2019.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Segun ya bayyana haka ne a shafinsa na Twitter, inda yace “Ga asusun neman taimako ga masu ra’ayin taimaka ma Atiku Abubakar don ya kwato hakkinsa daga wajen Buhari a gaban kotu, kuna iya tara kudinku anan.”

KU KARANTA: Shugaban majalisar dattawa: Sanatocin APC sun mika ma Buhari wuka da nama

Idan za’a tuna Atiku Abubakar ya sha kayi a hannun shugaban kasa Muhammadu Buhari a zaben shugaban kasar Najeriya daya gudana a ranar 23 ga watan Satumba, inda Buhari yaba Atiku tazarar kuri’u miliyan hudu.

Sai dai Atikun ya nuna rashin amincewarsa da sakamakon zaben da hukumar zabe mai zaman kanta INEC ta sanar, inda ya dauki alwashin kalulabantar sakamakon zaben a gaban kuliya manta sabo, har sai ya kwato hakkinsa daga wajen Buhari.

Atiku ya danganta rashin amimcewarsa da sakamakon ga yawan masu kada kuri’a da aka samu a jihohin dake yankin Arewa maso gabas, yankin da Buhari keda dimbin masoya da magoya baya da suka bashi mamakon kuri’u.

Don haka Atiku ya nuna damuwarsa da yadda za ace an samu yawan kuri’u a yankin duk kuwa da cewa akwai matsalar tsaro da ta dabaibaye yankin, fiye da sauran yankunan jihohin Najeriya da basu da irin wannan matsala, dalilinsa kenan.

Ana neman dala dubu dari, $100,000 ta wannan asusun tallafi, amma zuwa yanzu dala dari takwas da talatin da biyu, $832, kacal aka samu daga ranar Litinin, da aka bude asusun, Mista Segun Awosanya ya kara da cewa;

“Manufarmu mu saka kudadenmu a inda zamu kawar da zalunci da magudin zabe ta hanyar bada gudunmuwa a shari’ar da mukeyi da hukumar INEC da jam’iyyar APC.”

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel