Ka yarda da ikon Allah - Sarakunan gargajiya sun shawarci Atiku

Ka yarda da ikon Allah - Sarakunan gargajiya sun shawarci Atiku

Kungiyar masu sarautun gargajiya na kasa (NCTRN) ta shawarci dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar Peoples Democratic Party (PDP), ya amince da sakamakon zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar 23 ga watan Fabrairu.

Sarakunan gargajiyan sunyi wannan jawabin ne a ranar Talata yayin da suka ziyarci Shugba Muhammadu Buhari a fadar gwamnati na Aso Rock da ke Abuja.

Tawagar da Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa'ad Abubakar III na uku ya jagoranta ta bukaci Shugaba Buhari ya kasance mai gaskiya da adalci a cikin jagoracin kasar da ya keyi.

DUBA WANNAN: Tarihi: Kyawawan hotunan shugabannin Najeriya 5 da matan su

Ka yarda da ikon Allah - Sarakunan gargajiya sun shawarci Atiku
Ka yarda da ikon Allah - Sarakunan gargajiya sun shawarci Atiku
Asali: Twitter

Sultan ya tabbatar wa Buhari cewa za su bashi dukkan goyon bayan da ya ke bukata a yayin mulkinsa na shekaru hudu da zai yi nan gaba.

Ya ce: "Dukkan 'yan Najeriya su amince da sakamakon zaben a matsayin kaddara ta Allah. Allah ne ya kaddara za kayi tazarce kuma babu wanda zai iya canja hakan. Haka Allah ya kaddara saboda haka mun ziyarce ka ne domin mu baka goyon baya domin samar da zaman lafiya da cigaba a kasar mu."

A bangarensa, Oba Adeyeye Ogunwusi Ojaja II, Ooni na Ife kuma shima shugaba na kungiyar ya tabbatarwa Buhari cewa 'yan kungiyar za suyi aiki tare da shi domin kawar da miyagun ayyuka a kasar.

Buhari ya roki kungiyar suyi aiki tare da gwamnatinsa domin kawo cigaba a kasa baki daya.

"Kun san dukkan gidajen da ake boye masu laifi kuma kun san gidajen da akwai yara na gari. Kune kuka san abubuwan da ke faruwa a lungu da sako na garuruwa. Muna bukatar goyon bayan ku domin cigaba da ayyukan alheri da muka fara," inji shi.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel