Buhari zai rage ratar da ke tsakanin Mai kudi da Talaka – Inji Matar sa

Buhari zai rage ratar da ke tsakanin Mai kudi da Talaka – Inji Matar sa

- Hajiya Aisha Buhari tace sam Shugaba Buhari ba zai yi kasa a gwiwa ba

- Matar Shugaban kasar tace Gwamnatin ta APC za ta cika alkawuran ta

- Bayan nan kuma Hajiya Buhari tace za a dama mulki da Matasa yanzu

Buhari zai rage ratar da ke tsakanin Mai kudi da Talaka – Inji Matar sa
Buhari zai tafi da Matasa a karon nan inji Matar sa Aisha Buhari
Asali: Twitter

Mun ji cewa Uwargidar shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari watau Hajiya Aisha Buhari, ta tabbatarwa mutanen kasar nan cewa gwamnatin Mai gidan na ta zai kata kokari kan abin da yayi a baya a wannan karo.

Hajiya Aisha M. Buhari tace shugaban kasan zai rage ratar da ke tsakanin Attajirai da Fakirai a Najeriya. Hajiya Buhari ta kuma ce a wannan wa’adin, gwamnatin ta Buhari za ta cika duk manyan alkawuran da ta dauka a baya.

KU KARANTA: Manyan abubuwa da za su faru a Gwamnatin Buhari nan da 2023

Shugaba Muhammadu Buhari yayi alkawarin inganta tattalin arzikin Najeriya da yakar Barayi masu yi wa kasa zagon kasa, tare da kuma habaka sha’anin tsaro. Buhari tayi wannna jawabi ne jiya a fadar shugaban kasa.

Mai dakin shugaban kasar ta shiryawa wadanda su ka taya Mai gidan na ta samun nasarar lashe zaben 2019 wata gagarumar liyafa ne domin nuna godiyar ta. Aisha Buhari tace Matasa da ‘Yan mata sun bada gudumuwa sosai.

Uwargidar shugaban kasar ta jaddada shirin gwamnatin na APC na damawa da Matasa da ‘Yan mata wanda su ne su ka fi yawa a cikin al’umma a wannan tafiya. Buhari ta kuma ce shugaban kasar ba zai ba mutane kunya ba.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Shafin NAIJ Hausa ya koma LEGIT

Asali: Legit.ng

Online view pixel