Gobara ta hallaka wani Magidanci, Mai dakinsa da 'ya'yan sa 3 a jihar Kano
Tsautsayi da masu iya magana su ka ce ba ya wuce ranar sa ya auku a daren yau na Lahadi cikin Unguwar Hausawa daura da hanyar Bawo yayin da wutar gobara ta lakume wani Miji da Mata da kuma 'ya'yan su uku a birnin Kanon Dabo.
Kamar yadda majiyar jaridar Legit.ng ta ruwaito, wutar gobarar ta yi sanadiyar salwantar rayukan wani Magidanci, Isaiah Jonathan, Mai dakinsa, 'ya'yan su uku da kuma wata kanwa Matar sa da ajali ya katse ma su hanzari ba bu shiri.

Asali: UGC
Wani mashaidin wannan mugun ji da mugun gani yayin ganawa da manema labarai na jaridar The Cable ya bayyana cewa, aukuwar mummunar annobar da ta fara lakume ɗakin su na shakatawa ta haramta ma su hanyar neman tsira da a dole suka saduda su na ji su na gani.
Kakakin rundunar 'yan sandan jihar Kano, Abdullahi Kiyawa, cin bayyan damuwar sa gami da tausayi ya tabbatar da aukuwar wannan mummunan lamari kamar yadda shafin jaridar Vanguard ya ruwaito.
KARANTA KUMA: Nasarar Buhari ta kwantar da hankalin Ma'aikatan NNPC - Ughamadu
Cikin wani rahoton mai nasaba da wannan kamar yadda shafin jaridar BBC Hausa ya ruwaito, wata wutar gobara mai ci tamkar wutar Daji ta hallaka Mutane 78 a birnin Dhaka mai tsohon tarihi na kasar Bangalades.
Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa
Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:
https://facebook.com/legitnghausa
https://twitter.com/legitnghausa
Asali: Legit.ng