San barka: Manyan kasashen Duniya 11 da suka aiko ma Buhari da sakonnin taya murna

San barka: Manyan kasashen Duniya 11 da suka aiko ma Buhari da sakonnin taya murna

Tun bayan nasarar da shugaban kasar Najeriya Muhammadu Buhari ya samu a babban zaben kasar inda ya kayar da babban abokin hamayyarsa a zaben shugaban kasa, Alhaji Atiku Abubakar, kasashen duniya keta rige rigen tayashi murna.

Legit.ng ta ruwaito kasa ta farko data fara taya shugaba Buhari murnar samun nasara itace kasar China, inda shugaban kasar China, Xi Jin Ping ta bakin kaakakin ma’aikatan kula da harkokin kasashen Afirka ta kasar, Lu Kang ya taya Buhari murnar samun nasara, inda yace China na ganin girman Najeriya matuka.

KU KARANTA: Ahmed Musa ya taka rawar murnar nasarar shugaba Buhari

Sauran shuwagabannin kasashen da suka taya Muhammadu Buhari murnar tazarce akan kujerar shugaban kasa Najeriya sun hada da:

- Nana Akufo Addo na Ghana

- Emmerson Manangwagwa na Zimbabwe

- Macky Sall na kasar Senegal

- Mahamadou Issoufou na Nijar

- Sarki Mohammed Hassan na Morocco

- Alpha Conde na Guinea

- Theresa May ta Birtaniya

- Donald Trump na Amurka

- Uhuru Kenyatta na kasar Kenya

- Cyril Ramaphosa na Afirka ta kudu

Wannan shine zangon mulki na karshe da shugaba Buhari zai yi yana mulkin Najeriya, kuma Buharin mai shekaru 76 a duniya ya samu kashi 55.6 na kuri’un da aka kada yayin da Atiku Abubakar mai shekaru 73 na jam’iyyar PDP ya samu kaso 41.2.

Sai dai Atikun yace ba zai taba amincewa da sakamakon zabenba, inda yace ya shirya tsaf domin garzayawa gaban kotu don kwatar hakkinsa daga wajen Buhari sakamakon zargin magudi da aringizon kuri’a da yace jam’iyyar APC ta yi.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel