Masu tayar da zaune tsaye a jihar Sakkwato, Kaduna su kuka da kansu - Buhari

Masu tayar da zaune tsaye a jihar Sakkwato, Kaduna su kuka da kansu - Buhari

Biyo bayan samun nasarar sa, shugaban kasa Muhammadu Buhari, ya jajantawa 'yan uwan wadanda mummunan ta'addancin masu ta'ada ya ritsa da su cikin garuruwan Sakkwato da kuma Kaduna a kwana-kwanan nan.

A kwana-kwanan nan mun samu cewa, mummunan ta'addanci masu ta'ada a jihar Sakkawato da kuma rikici na kabilanci da ya auku a jihar Kaduna ya salwantar da rayukan mutane da dama kamar yadda shafin jaridar Daily Trust ya ruwaito.

Masu tayar da zaune tsaye a jihar Sakkwato, Kaduna su kuka da kansu - Buhari
Masu tayar da zaune tsaye a jihar Sakkwato, Kaduna su kuka da kansu - Buhari
Asali: UGC

Shugaban kasa Muhammadu Buhari cikin wata sanarwa da sa hannun mai magana, Mallam Garba Shehu, ya bayyana cewa, masu tayar da zaune tsaye gami da dabbaka ta'addanci akan al'umma su kuka da kawunan sa domin kuwa fushin hukuma ba zai rangwanta masu ba.

Cikin jawaban sa na jaddada muhimmancin rayuwar al'ummar kasar nan, shugaban kasa Buhari ya ce sauran kiris masu mummunar ta'ada su fuskanci makomarsu daidai da miyagun ababe da suke aikawata.

KARANTA KUMA: Sabuwar gwamnatin mu za ta kara kaimi wajen tsananta tsaro, habaka tattalin arziki, yakar cin hanci da rashawa - Buhari

Biyo bayan samun nasarar sa ta lashe zaben shugaban kasa da aka gudanar a ranar Asabar, 23, ga watan fabariraun 2019, shugaban kasa Buhari ya ce daukan matakai masu tsananin gaske wajen tsananta tsaro na daya daga cikin ababe da sabuwar gwamnatin sa za ta bai wa muhimmanci.

Jaridar Legit.ng ta ruwaito cewa, shugaban kasa Buhari cikin jawaban sa na bayyana farin cikin samun nasarar sa, ya ce gwamnatin sa za ta zage dantse wajen habaka tattalin arziki, tsananta harkokin tsaro da kuma tumke damara wajen yakar cin hanci da rashawa.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo cikin shafukan mu na zaurukan sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel