Mummunan kisa: Uwargida ta tuntsuro Maigidanta daga gidan sama a jahar Kano

Mummunan kisa: Uwargida ta tuntsuro Maigidanta daga gidan sama a jahar Kano

Rundunar Yansandan jahar Kano ta sanar da kama wata mata mai suna Rashida Muhammad da zargin laifin halaka Mijinta mai suna Adamu Ali a gidansu dake rukunin gidaje na Dorayi, cikin garin Kano.

Majiyar Legit.ng ta ruwaito Rashida ta halaka mijinnata ne ta hanyar tunkudashi daga gidan sama, inda yayi gangarowa akan matattakalan gidan sama, koda ya fado kasa haka tuni yace ga garinku nan.

KU KARANTA: Gumi ya shawarci Atiku ya garzaya kotu don kwatar mulki daga hannun Buhari

Kaakakin rundunar Yansandan jahar Kano, DSP Abdullahi Haruna ne ya tabbatar da aukuwar wannan lamari, inda yace lamarin ya faru ne da misalin karfe 8 na daren Litinin, 25 ga watan Feburairu, amma sai a ranar Talata suka samu nasarar cafketa.

Da yake jawabin yadda lamarin ya faru, DSP Haruna yace: “Rashida ta zargi mijinta yana waya da wata budurwarsa a cikin dakinsu ne, inda tayi kokarin kwace wayar tasa don tabbatar ma kanta, daga nan suka fara fada.

“Ana cikin haka ne sai Rashida ta tunkuda mijinnata daga saman matattakalan gidan saman, a haga yayi ta walagigi har sai dsaya tuntsuro kasa, koda aka duba shi sai aka tabbatar da ya mutu tun bayan tuntsurowarsa daga saman nan.” Inji shi.

Kaakakin yace zuwa yanzu an gudanar da jana’iza akan gawar mamacin tun bayan tabbatar da mutuwarsa a babban asibitin koyarwa na Malam Aminu Kano, sa’annan yace tuni sun kaddamar da binciken akan lamarin.

Daga karshe kaakakin rundunar Yansandan ta jahar Kano ya tabbatar da cewar zasu gurfanar da Rashin Muhammad gaban kuliya manta sabo da zarar sun kammala gudanar da cikakken bincike akanta.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel