Kalau na ke - Buba Galadima ya aike wasika ga iyalan sa

Kalau na ke - Buba Galadima ya aike wasika ga iyalan sa

A jiya ne iyalan Kakakin dan takarar shugabancin kasa na babban jam'iyyar adawa, Alhaji Buba Galadima sun ce sun samu wasika da aka ce wai shine ya rubuta daga wani wurin da bai bayyana ba.

An dai ce wai jami'an rundunar farar hula da DSS ne suka yi awon gaba da Galadima, mai magana da yawun dan takarar shugabancin kasa na jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar.

A jiya Talata 26 ga watan Fabrairu, mai dakinsa, Hajiya Fanna Galadima ta shaidawa Daily Trust cewa an aike musu da wasika misalin karfe shida na safe da aka rubuta da biro dauke da saka hannun mijinta inda ya tabbatar musu da cewa lafiyarsa kalau.

DUBA WANNAN: Yadda Buhari ya yi murdiyya wajen lashe zaben 2019 - Sheikh Ahmad Gumi

Kalau na ke - Buba Galadima ya aike wasika ga iyalan sa
Kalau na ke - Buba Galadima ya aike wasika ga iyalan sa
Asali: UGC

A hirar da ya yi da majiyar Legit.ng da suka ziyarci gidan Galadima da ke Wuse II a Abuja, yaronsa Dr Shettima Galadima ya ce wani mutum da ba su gane ko wanene ba ya kawo wasikar.

A cikin wasikar ta Buba Galadima, ya fada musu cewa kada su tayar da hankulansu amma bai bayyana inda ya ke ba a halin yanzu.

A yayin da ta ke bayanin yadda aka kama mijinta, Hajiya Fanna ta ce wata mota mara lamba ta rika sintiri a unguwarsu kafin daga bisani ta tsaya a gaban gidan.

Ta ce bayan lokaci kadan sai mijinta ya tuka motarsa ya fito daga gida kuma dai daga baya suka samu sakon cewa an kama shi.

Ta ce duk da cewa wasikar ta nuna cewa kada su damu, har yanzu suna cikin dimuwa tunda ba su san inda ake rike da mijin ta ba.

Sai dai Kakakin hukumar DSS, Peter Afunanya ya ce musanta cewa sune suka kama Buba Galadima.

Kazalika, Kakakin 'yan sandan Najeriya, DCP Frank Mba ya ce hukumar 'yan sanda ba ta da masaniya a kan kama Galadima.

An ruwaito cewa wasu mutane da suka rufe fuskokinsu ne suka yi awon gaba dashi a ranar Lahadi sa'o'i 24 kafin zaben shugaban kasa da na 'yan majalisun tarayya.

Mai magana da yawun kungiyar yakin neman zaben Buhari, Festus Keyamo ya fitar da sanarwa inda ya nemi a kama Galadima saboda yana shirin yada labaran karya game da zaben na 2019.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel